Sarkin Kano Ne Zai Jagoranci Sallar Jumu'a---'yan sanda

Sarkin Kano Ne Zai Jagoranci Sallar Jumu'a---'yan sanda

Rundunar 'yan sandan Kano sun bayyana cewa Sarkin Kano na 16 Sanusi Lamido ll ne zai jagoranci sallar juma'a a babban masallacin Kano.

Bayanin ya fito ne bayan labarin da ake yawo da shi a kafafen sada zumunta Alhaji Aminu Ado Bayero Sarkin Kano na 15 zai jagoranci Sallah a masallacin.

Kwamishinan 'yan sanda Hussaini Gumel  ya sanar da kafar yada labarai ta NAN a wayar tarho Bayero zai yi sallarsa a fadar Nasarawa in da yake zaune a halin yanzu.