Sanata Wamakko Ya Kashe Miliyan 800 Ga 'Yan Asalin Sakkwato 600

Sanata Wamakko Ya Kashe Miliyan 800 Ga 'Yan Asalin Sakkwato 600
 

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya kashe kudi sama da miliyan 800 domin daukar nauyin karatun dalibbai 'yan asalin jihar Sakkwato su 600  tun daga 2015 zuwa yau.

Daraktan Mulki na Sanata Wamakko, Alhaji Mustapha Abubakar  Alkali ne ya sanar da manema labarai a satin da yagabata ya ce Sanatan ya daukin nauyin wasu dalibai su 17 su yi karatun digiri na farko a jami'ar Lahore dake jamhuriyar Pakistan.  
Ya ce Sanata Wamakko ya dauki nauyin da yawan yara a Sakkwato don su yi karatun digiri na farko dana biyu dana uku a ciki da wajen Nijeriya da yawansu zai kai 600 in da aka kashe masu kudi sama da miliyan 800.
"Na baya bayan nan dalibai 17 da aka tura Pakistan don su karanto Injiniya da kwasakwasan kimiya da fasahar sadarwa da sauransu.
"Dalibban farko su 25 da aka tura a Pakistan sun kammala karatunsu da sakamako mai kyau." 
Ya ce Sanatan ya tura wasu mutum uku a USA da wasu 4 a UK da wasu 4 Cyprus da wasu 3 Malaysia da 13 a Bangladesh da wasu 89 a Maradi haka dai yawansu a wurare da dama.
Mustapha ya ce wannan kokarin an samar da shi ne domin samun cigaban a hajin ilmi a Sakkwato musamman ga 'ya'yan talakawa su zama ana iya gogawa da su a kasar Nijeriya.
anata Wamakko da yake wakiltar yankin Sakkwato ta tsakiya a majalisar dattijai ya ce ya yi kokarin tallafawa matasa domin su zama masu cin gashin kansu ya kuma raba na'urar raba wutar lantarki waton Taranfoma sama da guda 100 bayan gina ajujuwan makaranta da taimakon marayu.