Sanata Lawan ya tallafa wa yan kasuwar Nguru da N100m
Daga Muhammad Maitela, Damaturu.
Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Ibrahim Lawan ya tallafa wa yan kasuwar Nguru da ke jihar Yobe da kyautar naira miliyan 100 don habaka harkokin kasuwanci da samar da ayyukan yi a yankin.
Sanatan ya bayyana hakan yau Asabar, a lokacin bikin bude sabuwar kasuwar zamani da gwamnatin jihar Yobe ta gina a garin, wadda aka sanya wa sunan Sheikh Muhammad Ngibrima Modern Market.
Haka kuma ya yaba wa kokarin gwamnatin jihar da ta samar da muhimman ayyukan ci gaba da bunkasa harkokin tattalin arziki a yankin, ya ce, "Gwamnatin jihar Yobe ta nuna mana kauna da kishi wajen samar da wadannan muhimman ayyukan ci gaba, wanda zasu zasu inganta rayuwar matasa da al'umma baki daya."
"Saboda haka, a karkashin gidauniyar SAIL Foundation, zan bayar da tawa gudumawa ta naira miliyan 100 ga yan kasuwar Nguru. A baya na bai wa yan kasuwar Yobe ta Arewa tallafin naira miliyan 200 ga kananan yan kasuwa 40 kowane naira 500,000 don habaka kasuwanci." In ji shi.
A nashi jawabin, Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta samar da kasuwannin zamani biyar a manyan garuruwa; Damaturu, Potiskum, Gashu'a da Nguru domin inganta harkokin Kasuwanci da samarwa matass aikin yi.
"Idan zaku tuna, ranar 19 ga watan Uktoban 2020 muka bayar da kwangilar aikin kasuwar Nguru kan naira biliyan uku da digo 8 (N3.8bn) wanda ta kunshi shaguna 505, bangaren gudanarwa, rijiyar burtsatse, masallaci da ofishin wutar lantarki, da sauran kayan alatu da makamantan su."
"Zan yi amfani da wannan dama wajen yaba wa dan kwangilar da ya gudanar da aikin cikin lokaci, wanda hakan ya bamu damar kaddamar da bude kasuwa, wadda muka sanya wa sabuwar kasuwar sunan Sheikh Muhammad Ngibrima Modern Market."
Gwamna Buni ya kara da cewa, gwamnatin jihar ta yanke shawarar sanya sunan Sheikh Muhammad Ngibrima ne saboda sadaukarwar sa a hidima ga addinin musulunci tare da gudanar da rayuwarsa wajen kira tare da koyar da ilimin addinin musulunci, wanda ya taimaka wajen fito da sunan jihar Yobe aka santa a ko'ina.
Bugu da kari kuma, Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya shi ne ya jagoranci bude sabuwar kasuwar zamanin, wadda gwamnatin jihar Yobe ta gina.
managarciya