Sanata Ibrahim Lamido ya yi ta’aziyar rasuwar tsohon mataimakin gwamnan Sakkwato Alhaji Ahmad Muhammad Gusau wanda ya rasu a jiya Jumu’a, bayan fama da doguwar jinya.
Sanata Lamido a bayanin da ya fitar da kansa ya mika sakon ta’aziyar ga iyalai da masoya da mutanen Sakkwato baki daya.
Sanata ya bayyana marigayin a lokacin rayuwarsa mutum ne karimci da sakin fuska da son gaskiya a harkokinsa, ya roki Allah ya gafarta masa.
Ibrahim Lamido ya ce marigayi ya bar giɓi mai wuyar cikewa kan haka ya roki iyalai da su jure kan rashin da aka yi a jiha da kasa baki daya.





