Sanata Lamido Ya Jajantawa Mutanen Gwadabawa da Gatawa Kan Harin ‘Yan Bindiga a Sakkwato

Sanata Lamido Ya Jajantawa Mutanen Gwadabawa da Gatawa Kan Harin ‘Yan Bindiga a Sakkwato

Sanata Ibrahim Lamido ya jajantawa al’ummar garin Gwadabawa da Gatawa kan harin da ‘yan bindiga da suka kai masu satin nan a cikin al’ummominsu daban-daban.

Sanata Ibrahim Lamido da yake tir da lamarin a ranar Lahadin data gabata ya bayyana lamarin abin da ba za su rungumi hannu suna kallonsa ba ne, za a kara daukar matakan da suka dace.

A bayanin da ofishin yada labarai na Sanata Ibrahim Lamido ya fitar ya jajantawa iyalai da mutanen Gwadabawa da mutanen Sakkwato gaba daya kan musibar da ta faru, ya kuma ba su tabbacin gwamnatin Sakkwato za ta kara daukar matakan da suka dace domin kare rayuwa da dukiyoyin jama'a.

Haka ma Lamido ya yi ta’aziya ga mutanen Gatawa a karamar hukumar Sabon Birni kan mutanen da ‘yan bindiga suka kashe ba tare da hakki ba.

Ya roki Allah ya gafartwa mutanen da suka rasa rayukkansu,  iyalansu kuma ya ba su hakirin jure rashinsu.