Home Siyasa Sanata Hanga ya Fara yunƙurin ficewa daga Kwankwasiyya

Sanata Hanga ya Fara yunƙurin ficewa daga Kwankwasiyya

14
0

Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya Sanata Rufa’i Hanga ya soma jin ra’ayin magoya bayansa kan ci gaba da zama ko barin tsarin Kwankwasiyya.

Arewa Updates ta rawaito cewa, hakan ya biyo bayan taron masu ruwa da tsaki na magoya bayansa.

Yayin ganawar ɗansa Samir Rufaʼi Hanga ya yi kira da magoya bayan su koma mazaɓu da ƙananan hukumominsu su tattauna da sauran mabiya don jin raʼayinsu kan ci gaba da zama a Kwankwasiyya ko kuma a tsallaka titi.

Ya ce, a halin yanzu ADC da APC sai zawarcin Sanatan su ke yi.

Samir ya ce, za su duba inda suka ga suna da mutunci a wajen, kuma ina ne mutanensu za su samu makoma.

A cewarsa, bayan haka za su gabatar wa da Sanatan shawarar ƙarshe domin ɗaukar matsaya.

Samir ya jaddada cewa, za a tabbatar an yi tsari mai kyau da za a rika tafiya tare da kowa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here