Sanata Adamu Aliero Yana Cikin 'Yan Majalisar Dattawa Da Zasu Yi Bankwana Da Majalisar Dokokin Najeriya

Sanata Adamu Aliero Yana Cikin 'Yan Majalisar Dattawa Da Zasu Yi Bankwana Da Majalisar Dokokin Najeriya
 

Daga Abbakar Aleeyu Anache.

 

Wannan na zuwa ne bayan wani hukunci da kotun daukaka kara a Sokoto ta yanke na hana tsohon gwamnan jihar Kebbi Sanata Adamu Aliero da tsohon jagoran majalisar dattawa Sanata Yahaya Abdullahi yin takarar kujerun Sanata a zaben 2023. 

 

Rikicin takarar kujerun Sanatoci na jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya na zuwa ne bayan komawa jam'iyyar PDP da tsohon gwamnan jihar Sanata Adamu Aliero da tsohon jagoran majalisar dattawa Sanata Yahaya Abdullahi suka yi bayan da jam'iyyar ta riga ta kammala zabukan fitar da yan takara, 
 
Jam'iyyar PDP a jihar Kebbi ta sake gudanar da zabukan tsayar da yan takara a wasu mazabu inda aka zabi Adamu Aliero a matsayin dan takarar Sanatan Kebbi ta tsakiya bayan da Haruna Sa'idu ne ya ci zaben na farko inda kuma ta tsayar da Yahaya Abdullahi dan takarar Sanatan Kebbi ta arewa,
 
An shigar da karar Sanatocin biyu inda babbar kotun tarayya da ke Birnin Kebbi ta bai wa Haruna Sa'idu takarar Kebbi ta tsakiya shi kuma Sani Bawa Argungu aka bashi takarar Kebbi ta arewa sai dai Adamu Aliero da Yahaya Abdullahi basu amince da hukuncin ba suka daukaka kara,
 
A hukuncin da alkalan kotun daukaka kara su uku suka yanke wanda mai shari'a Muhammad Danjuma ya karanta kotun ta yi watsi da daukaka karar inda ta tabbatar da hukuncin kotu na farko, 
 
Jagoran lauyoyin masu daukaka kara Barista Illo Katune Sanusi yace zasu yi nazarin hukuncin da kotun ta yi kuma zasu dauki matakin zuwa kotu ta gaba, 
 
Shi kuwa daya daga cikin lauyoyin wadanda ake kara Muhammad Mansur Aliyu cewa yayi an yi hukuncin cikin adalci,