Samar Da Wurin Wasa Na Zamani A Sakkwato:Wamakko Ya Yabawa Dan Kwallon Nijeriya

Samar Da Wurin Wasa Na Zamani A Sakkwato:Wamakko Ya Yabawa Dan Kwallon Nijeriya

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya yabawa dan kwallon Nijeriya Abdullahi Shehu kan samar da filin wasa na zamani irinsa na farko a jiharsa ta haihuwa domin bunkasa harkokin wasanni da samar da aikin yi ga matasa.

Sanata Wamakko ya bayyana hakan a lokacin da ya ziyarci katafaren wurin da ake kan ginawa domin sanya albarkarsa a matsayinsa na daya daga cikin jagororin matasa a jihar Sakkwato.

Ya ce wannan wurin da ka samara bin yabawa ne da ake son duk wani dan kasa mai kirki da son cigaban jama’arsa ya yi domin bunkasar jiha da kasa baki daya.

Tsohon gwamna na Sakkwato  ya ce “Wannan wurin zai taimakawa al’ummar Sakkwato da Nijeriya gaba daya, duk wanda ya samu wata baiwa akwai bukatar ya taimaki addini da al’umma ba shi kadai ba, dan kasa mai kirki idan ya samu jama’a za ta amfana ta hanyar samun cigaba.

“Wannan wurin dubban matasa za su samu aikin yi, gari zai samu Karin  daukaka, kalubale ne ga matasan jihar nan,  da yawanku kuna da basirar taka leda duk wanda yake da sha’awar buga kwallon kafa  ya yi amma ya hada da irin wannan cigaban don kar abar wasannin baya, motsa jiki na da muhimmanci a lafiyar mutum da addini,”  a cewar Sanata Wamakko.

Da farko Dan wasan a kungiyar kwallon kafa ta Nijeriya ya zagaya da ayarin Sanatan domin nuna masu cigaban da aka samar a wurin wanda zai kawo cigaban jihar matasa kuma su yi alfahari da shi.