Sallah sai Laraba a Nijeriya---Sarkin Musulmi

Sallah sai Laraba a Nijeriya---Sarkin Musulmi


Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya sanar da cigaba da yin Azumin Ramadan a Nijeriya gobe Talata  ganin ba a samu labarin ganin Watan Sawwal ba, sallah sai zuwa ranar Laraba.
Sarkin Musulmi ya yi kira ga al'ummar Musulmi da su cigaba da yin ibadodi da aiyukkan alheri  don samun zaman lafiya, aminci da kwanciyar hankali da samun sauki.
Ya yi kira da a yi wa shugabanni addu'a Allah ya aza su kan abubuwan da za su Kawo maslaha da alheri a kasar Nijeriya.