Salame Tare da hadin guiwar Gidauniyar Farida Sun koyar da mata 557 a Sakkwato

Salame Tare da hadin guiwar Gidauniyar Farida Sun koyar da mata 557 a Sakkwato

Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Gwadabawa da Illela Honarabul Abdullahi Balarabe Salame  ya daukin nauyin koyar da mata akalla 557 sana'o'in dogaro da kai a jihar Sakkwato.

Horaswar tana tare da hadin guiwar Gidauniyar Farida waton FLONY da ta bayar da horon sana'o'in samar da  filo da dardumar  alfarma da kayan kwalliya da Kek da sauransu.
Bayan kammala horaswar ta sati daya Dan majalisar ya bayyana farincikinsa kan wannan hobbasar da takai ga matasa domin su samu abin da za su gina kansu.
Salame ya ce wannan horaswa tana cikin aiyukkan da shugaban kasa Buhari ke bukatar a aiwatar ga talakawa domin magance masu fatara da zaman kashe wando.
Ya ce abin da wannan gidauniyar ke yi abin yabawa ne, aikinta ya game ko'ina a Nijeriya ba tare da wani dogon surutu ba.
Ya yi kira ga matasan da aka koyar kar su yi wasa da abin da suka koya su rike shi da hannu biyu domin dogaro da kai, da taimakawa gida,
Hajiya Farida Jauro shugabar Gidauniyar FLONY ta kasa ta bayyyana farincikinta ga yanda aka samu nasarar horasda dimbin mutane a kankanen lokaci suka kware har suke iya samar da kayan da ake bukata kai tsaye.
Wadan da aka horaswa kusan dukansu mata ne su samu horo kan computer da kayan kwaliya da sauran kayan amfanin gida.