Home Rahoto Sakon Sakatare Janar Na MDD Na Murnar Fara Azumin Ramadan 2026

Sakon Sakatare Janar Na MDD Na Murnar Fara Azumin Ramadan 2026

6
0

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya fitar da sakon taɓa zuciya domin murnar fara watan Ramadan na Shekarar 2026 a inda ya yi kira ga duniya baki ɗaya da ta rungumi ruhin zaman lafiya, tausayi da haɗin kai da wannan wata mai tsarki ke ɗauke da shi.

A cikin sakon nasa, Guterres ya jaddada cewa Ramadan ba lokaci ne na ibada da tunani kawai ba, wata ce ta ƙarfafa bege da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Ya yi kira ga kowa da kowa da ya yi amfani da wannan lokaci wajen ƙarfafa haɗin kai da kuma nuna kulawa ga masu fama da rashin zaman lafiya a kasashe daban-daban na duniya.

“Ga Musulmai a duk faɗin duniya, watan Ramadan mai tsarki lokaci ne na tunani da addu’a.

“Ramadan kuma yana wakiltar zaman lafiya.”

Mista Antonio ya yi nuni da rikice-rikicen da ke ci gaba da addabar al’umma a kasashe daban-daban na duniya. Ya bayyana cewa an Afghanistan, Yemen, Gaza, Sudan da kuma wasu wurare, miliyoyin mutane na fuskantar “munanan tasirin rikici, yunwa, ƙaura, wariya da sauran matsaloli.”

“A cikin waɗannan lokuta masu wahala, mu saurari saƙon da Ramadan ke ɗauke da shi wanda ba ya gushewa.

“Don haɗa kan al’umma. Don kawo taimako da bege ga waɗanda ke cikin wahala. Kuma don kare haƙƙoƙi da mutuncin kowane mutum.”

Mista Antonio ya kara da cewa, “Kowace shekara, ina yin ziyara ta musamman zuwa al’ummar Musulmi masu azumi kuma ina buda baki da su. Kuma kowace shekara nakan dawo da kwarin gwiwa daga ruhin Ramadan na zaman lafiya da tausayi.

“Allah ya sa wannan wata Mai Tsarki ya zame mana abin da zai ƙarfafa mu mu yi aiki tare a matsayin ɗaya, domin gina duniya mai cike da zaman lafiya, karamci da adalci ga kowa da kowa.

“Ramadan Kareem”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here