Home Labarai Sakkwato za ta karɓi baƙi a Afirka domin taron Zakka da Waƙafi 

Sakkwato za ta karɓi baƙi a Afirka domin taron Zakka da Waƙafi 

37
0

Hukumar Zakka da wakafi ta jihara Sakkwato da bankin raya musulunci sun shirya taron bita da karawa juna sani kan aiyukkan zakka da wakafi da wasu shirararuwan bunkasa arziki da kasuwanci a tsakanin jama’a.

Taron zai karbi manyan malamai daga sassa daban daban a Saudiya da Afirika ta Yamma da Nijeriya don ganin an kara fito da ayukkan Zakka da Wakafi a zamanance domin tafiya da kowane hali da ake ciki.

Shugaban hukumar Malam Muhammad Lawal Maidoki ne ya sanar da taron a wani zama da manema labarai a Sakkwato ya ce za a kaa fito da bayani kan tattalin arziki da ilmin tattalin arziki na Musulunci don kara bunkasa ayyukkan Zakkah da wakafi musamman a Nijeriya.

Ya ce taron Afirka ta Yamma ne zai kara fita da ‘yan uwantaka bita ce taron wanda malamai a ƙasar Saudiyya za su zo domin ilmantar da mutane harkokin Zakka da Wakafi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here