Sakkwato: Akwai bambancin fahimta a tsakanin al'umma  kan harin jirgin soja

Sakkwato: Akwai bambancin fahimta a tsakanin al'umma  kan harin jirgin soja

Gwamnan Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu ya kai ziyarar ta'aziya a karamar hukumar Silame a satin da ya gabata in da jirgin Soja ya halaka mutum 10, shida sun jikkata kan zargin 'yan ta'addar Lakurawa ne, an yi sallar janaza da shi ya kai masu tallafi.

Gwamnan ya nuna kuskure ne lamarin da ya faru an kai harin ne domin halaka Lakurawa da ke yankin sai abin ya rutsa da mutanen yankin da ba su ji ba su gani ba.

Ana haka sai ga bayanai sun fito daga rundunar Soja cewa ba kuskure ba ne,  suna da bayanan akwai Lakurawa a yankin kuma su Lakurawa suka kashe ba su yi kuskure a abin da suka aiwatar ba, abin da mutane ke ganin akwai bambanci ra'ayi da fahimta kan abin da ya faru  

Barista Alkali Sidi ya ce “abin da wannan ke nufi dukan masu yaki da ta'adanci a Nijeriya ba su dauki shawarar shugaban kasa Tinubu ba na cewa a samu hadaka da aiki tare a tsakani wanda hakan shi ke kawo cikas ga fada da ta'adanci rashin fahimtar juna hakan ya sa mutane da dama suka zargi cewa akwai bara gurbi a jami'an tsaro da ke amfana da wannan matsalaar tsaro, wasu na ganin har da shigar kasashen waje don cimma wata manufa ta su.

"Jihohi ba su da hurumin yin doka ko wani tsari kan tsaro lamari ne na gwamnatin tarayya, amma tsarin dokar kasa tana gaban kowace doka ta hukuma, shi ne ya aiyana gwamna matsayin shugaban tsaro a jiharsa, ko da fada da 'yan ta'adda   ba aikin gwamna ba ne sanin matsalar da ke cikin jiharsa hakkinsa ne, bai kamata wannan samame a yi shi ba tare da sanin gwamna ba, sanar da gwamna ba shi ke nuna an bude sirrin tsaro ba. Bai kamata a ki sanar da shi ba sai ko in gwamna ya boyewa talakawansa ne.

"Maganar Gwamna kan kuskure ne aka yi, sojoji su ce dagangan suka yi, yakamata a koma kan biyayya ga tsarin doka, sabawa doka ne a kashe wadan nan mutane an ketare iyaka, duk wanda kake iya kamawa ko raunata shi doka ba ta aminta ka kashe shi ba," Kalaman Barista Sidi.

Muhammad Nasir yana ganin abu ne duk sanda ake shugabanci sai lamarin siyasa ya shigo ciki zuwan da gwamna ya yi ta'aziya don ya jajantawa al'ummarsa ne da yake mulka.

"Kalaman da ya yi ba su ne muka so ji ba mun so ya sanar da duniya kashin kuskure da aka yi ba zai je a banza ba, za a dauki mataki nan take domin wadan da aka kashe ba batagari ba ne don haka ya yi masu sallah, alhaki na wuyansa na kwato masu hakki.

"Bayan da sojoji suka yi magaana akwai bukatar gwamna ya yi masu martani kan matsayarsa ta farko don ya san al'ummarsa ce aka kashe basu ji ba su gani ba, a dauki lamarin da muhimmanci don jininsu kar ya tafi ga banza."

Farfesa Mu'azu Shamaki ya ce "ba mamaki irin wannan tun a da Nijeriya ne amma matsala anan muna wasa da shugabanci ne tun da abin Gwamna zai fadi tabbatacce ne don an yi nazari kansa, mu a wurin mu abin da ya faru gwamnan mu ya yi magana sojoji su karyata shi an ci zarafinmu reni ne ba mu ji dadi ba."