Ruwan sama ya hana ɗalibai  zuwa makaranta tsawon kwanaki 3 a Jigawa

Ruwan sama ya hana ɗalibai  zuwa makaranta tsawon kwanaki 3 a Jigawa
 
 

 

Mamakon ruwan sama da aka kwana 3 ana yi ya hana ɗaliban firamare zuwa makarantar har na tsawon kwanaki uku, tare kuma da jawo ruftawar banɗakuna da dama a garin Aujara dake Ƙaramar Hukumar Aujara ta jihar Jigawa.

 
Wani mazaunin garin na Aujara, mai suna Shamsudeen Bala Aujara, yace ruwa na shiga gidaje da dama kuma ya dakatar da duk harkokin yau da kullum a garin sakamakon yawan ruwan.
 
“Yanzu hakan ma kwanaki uku kenan daliban makarantar firamaren dake Aujara ba su samu damar zuwa makarantar ba, saboda yadda ruwan ya cika makarantar makil, inda hakan yayi sanadiyar dakatar da karatu a makarantar.
 
” Yanzu maganar da nake yi maka gidan Hakiminmu ma yanzu haka saboda yawan ruwa da ke taruwa a Kofar gidan ba’ a iya shige da fice a gidan tsawon waɗannan kwanaki uku”. inji shi
 
Yace akwai bukatar mahukunta a jihar ta Jigawa su kaiwa al’ummar garin dauki saboda mawuyacin halin da suke ciki, Inda yace akalla banɗakuna na gidaje fiye da 50 me su ka rufta cikin wannan kwanaki ukun.
 
Da ya ke bayani kan lamarin, Shugaban Ƙaramar Hukumar ta Aujara Ado Mai Unguwa Aujara yace suna iya bakin kokarisu don ganin sun samar da wasu injina da zasu rika zuke ruwan dake taruwa a makarantar don baiwa daliban damar zuwa makarantar.
 
Yace gwamnatin jihar Jigawa tana iya bakin kokarita don ganin an Samar da magudanan ruwa da kuma ɗaukar sauran matakai don gudun faruwar hakan a nan gaba.