Rikicin Sudan: Hukumar Alhazai Za Ta Rage Guzurin Mahajjatan Nijeriya

Rikicin Sudan: Hukumar Alhazai Za Ta Rage Guzurin Mahajjatan Nijeriya

Hukumar mahajjatan  Nijeriya ta sanar da alhazzan da za su yi aikin hajjin bana a shekarar 2023 tsare-tsaren tashi da kuma rage guzurinsu da za ta yi ba kamar yadda aka saba ba.

Hukumar mahajjatan a takardar da shugabanta Zikirullahi Kunle Hassan ya sanyawa hannu ya nemi sakataren zartarwa a hukumar Alhazai ta jihar Sakkwato da ya nasarwa mahajjatan jiha a cikin dala 800 da ake baiwa mahajjaci na guzuri a baya yanzu za a bashi dala 700 matsayin kudin rikewa da ake kira (B.T.A).

Bayanin ya nuna yanda kudin suka koma hakan saboda rikicin Sudan, tattalin arziki da harkokin jirgin sama.

Shugaban ya nemi da a sanarwa mahajjata wannan tsarin domin samun damar a yi aiki cikin lumana da nutsuwa.

Ya ce kamfanin jirage hudu ne za su yi aikin kwashe maniyatan Hajjin bana daga Nijeriya da suka hada Max, Aero, Air Peace da Azman.