Rikicin PDP: Dole Ayu ya sauka, in ji Gwamna Makinde

Rikicin PDP: Dole Ayu ya sauka, in ji Gwamna Makinde

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo a yau Larabar ya dage cewa dole ne Dr Iyorchia Ayu, shugaban jam’iyyar PDP na kasa ya sauka daga mukaminsa domin bai wa ƴan Kudu damar shiga manyan mukamai na jam’iyyar.

Makinde ya bayyana matsayin shugabannin jam’iyyar na Kudu-maso-Yamma a taron masu ruwa da tsaki na shiyyar da aka gudanar a ɗakin taro na Farfesa Theophilus Ogunlesi da ke Asibitin Kwalejin Jami’ar Ibadan.

A cewarsa, PDP na magana ne kan haɗin kan ƙasa, magana kan gwamnatin haɗin kan ƙasa.

“To, batun shi ne cewa dole ne mu yi abin da muke wa’azi a kai. Idan har muna son haɗa kan Najeriya, dole ne mu hada kan PDP tukuna.

“Idan muna son gwamnatin haɗin kan ƙasa, dole ne fuskokin PDP su nuna hadin kan kasa.

"Idan muna son sake fasalin Najeriya, dole ne mu kasance da shirye-shiryen yin abin da ya dace don kawo hadaka cikin PDP.

“Sakon jam’iyyar PDP ta Kudu-maso-Yamma shi ne a sake fasalin kwamitin gudanarwa na kasa na PDP.

“sabo da haka muna kira da shugaban jam'iyya na kasa da ya sauka daga mukaminsa domin a haɗin kan Kudu gaba daya. Wannan shi ne sakon,” in ji Makinde.

A nasa jawabin, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Abubakar Atiku, ya ce ya je Ibadan ne domin tattaunawa da dukkanin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar kan shirye-shiryen tunkarar zaben 2023.

 Atiku ya bukaci shugabannin jam’iyyar Kudu-maso-Yamma da su ci gaba da mayar da hankali wajen ganin jam’iyyar ta samu nasara a zabe mai zuwa.