Rikicin APC A  Kano: Tinubu Da Shekarau Sun Yi Ganawar Sirri A Legas

Rikicin APC A  Kano: Tinubu Da Shekarau Sun Yi Ganawar Sirri A Legas

Yayin da rikicin jam'iya mai mulki, APC ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a Jihar Kano, a na ta samun yunƙurin sasanta ɓangarorin da ke zaman doya da manja a jihar.
Bayan da kwamitin sulhu da APC ta kafa ya fara aiki a makon da ya gabata, inda ya yi iƙrarin cewa ya sulhunta tsakanin Gwamna mai ci, Abdullahi Ganduje da tsohon gwamna, Ibrahim Shekarau, alamu dai sun nuna cewa har yanzu a kwai sauran rina a kaba a game da dambarwar siyasar da ta dabaibaye jam'iyar a jihar.
Sai dai kuma, rahotanni sun nuna cewa, Jagoran APC na ƙasa, Bola Tinubu ya fara na shi yunƙurin na sasanta ɓangarori biyun a jam'iyar a Kano.

Jami'i mai kula da yada labarai na Tinubu, Mista Tunde Rahman ya tabbatar haɗuwar jagororin a garin Lagos.
Ɗaya daga cikin jagorori a tsagin Shekarau ya ce suna da damar ganawa da Tinubu domin su ne ke rike da jam'iya a Kano.

Har yanzu ba a ba da rahoton yanda tattaunawar ta gudana da dalilin yin hakan, amma dai haɗuwar ta zo bazata musamman mutane a ɓangaren Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.