Home Uncategorized Rikici ya ɓarke a kudancin Kaduna, har an kashe mutum 30 

Rikici ya ɓarke a kudancin Kaduna, har an kashe mutum 30 

3
0

Rikici ya ɓarke a kudancin Kaduna, har an kashe mutum 30 

Aƙalla mutum 30 suka mutu sannan an kona gidaje da dama a kauyukan Madamai da Abun na karamar hukumar Kaura da ke jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta rawaito tsohon shugaban kungiyar hadin-kan matasan Kaura, Kwamared Derek Christopher na cewa maharan sun kutsa yankunan da misali karfe 5 na yamma suka rinka harbe-harbe kan mai uwa dawabi.

Ya kuma shaida cewa yawancin mutanen da aka jikkata an kai su asibiti domin basu kulawa.

Rundunar ‘yan sanda Kaduna kawo yanzu ba ta ce komai a kan harin ba.

Daga: Comrade Musa Garba Augie.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here