Rijistara  Kotun Shari'ar Musulunci a Neja Ya Mutu  Hannun 'Yan Bindiga

Rijistara  Kotun Shari'ar Musulunci a Neja Ya Mutu  Hannun 'Yan Bindiga

 

Rijistara mai kula da dukkanin bayanan harkokin Kotun shari'ar Musulunci da ke Ibbi, karamar hukumar Mashegu a jihar Neja, Mallam Namaru, ya rasu. 

Daily Trust ta rahoto cewa 'yan bindiga ne suka kashe ma'aikacin Kotun Musuluncin mako biyu bayan sun yi garkuwa da shi a watan Ramadan.
Har yanzu babu cikakken bayani kan dalilin da yasa suka kashe Mallam Namaru amma City & Crimeta tattaro cewa yan bindiga sun sace mamacin tare da wasu ranar 24 ga watan Maris. 
Duk wani yunkurin samun jami'in hulɗa da jama'a na hukumar yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, kan batun kisan mutumin ya ci tura har kawo yanzu da muke haɗa rahoto. 
Amma wani mazaunin yankin, Abdullahi Abubakar, ya shaida wa wakilin jaridar cewa yan ta'addan sun bindige rijistaran da sauran waɗanda aka sace su tare saboda matsin lambar da suke sha daga jami'an tsaro. 
Ya ce jami'an tsaro sun matsa kaimi don ceto mutanen shiyasa masu garkuwan suka halaka su. 
Ya ce sanadiyyar haka aka harbe wani ɗan banga har lahira. 
Abubakar ya ce a halin yanzu ana ta kokarin ɗauko gawarwakin mutanen da aka kashe domin a musu Jana'iza da kuma ceto ragowar waɗanda ke raye Mutumin yace garin Ibbi da ake ganin akwai zaman lafiya kuma har masu gudun Hijira ke samun mafaka, a mako biyu da suka shige ya fara fuskantar hare-hare.