Rigimar APC:Shugaban 'Yan Sanda Ya Gayyaci Gefen Ganduje Da Shekarau

Rigimar APC:Shugaban 'Yan Sanda Ya Gayyaci Gefen Ganduje Da Shekarau
 

Shugaban 'Yan Sanda na Nijeriya Usman Alkali, ya gaiyace ɓangarorin da ke rikici a jam'iya mai mulki ta APC a Jihar Kano.

 

A  watannin da su ka gabata ne rikici ya ɓarke a APC a Kano, inda tuni jam'iyar ta dare gida biyu, lamarin da ya haifar da ɓangarori biyu a ƙarƙashin jagorancin Gwamna mai ci, Abdullahi Umar Ganduje da kuma tsohon gwamna, Sanata Ibrahim Shekarau.

 
Idan za a iya tunawa, ɓangaren Shekarau sun kai takardar ƙorafi zuwa ga ofishin Shugaban  ɗin, in da su ke zargin tsagin Ganduje da kai hari kan ofishin Sanata Barau Jibrin a Kano.
 
Nan da nan suma ɓangaren Ganduje su kai kai ƙarar tsagin Shekarau gaban Shugaban ɗin a bisa zargin su Shekarau ɗin da tada zaune tsaye a jihar.
 
Daily Nigerian Hausa ta gano cewa waɗannan ƙorafe-ƙorafe ne su ka sanya ya gaiyace su domin shawo kan matsalar.
 
Jaridar nan ta jiyo cewa tuni wakilan ɓangarorin su ka isa hidikwatar 'yan sandan dake gidan Louis Edet a Abuja yau Talata da safe.
Rigimar ta su kullum karuwa take yi duk da Gwamna Ganduje ya ce ba za su kawar masa da hankali a aiyukkan cigaban jiha da yake aiwatarwa ba.
Wasu na ganin wannan rigimar rashin adalci ne karara uwar jam'iyar APC ke kokarin yi wa Gandujen ganin ba wani gwamna da ake irin wannan rigima a jiharsa.
Gwamnan a taron masu ruwa da tsaki ya nuna wannan ba wani matsala ba ce domin siyasa ta gadi haka za a yi jayayya daga baya mai girma ya dauki abinsa.