Reni: Majalisar Dokoki ta sanya zare da Kwamishiniyar lafiya ta Sakkwato 

Reni: Majalisar Dokoki ta sanya zare da Kwamishiniyar lafiya ta Sakkwato 

Majalisar dokokin jihar Sakkwato ta gayyaci kwamishiniyar lafiya ta jiha Hajiya Asabe Balarabe da  ta bayyana gaban kwamiti a ranar Talata bayan ta bijirewa gayyatar da aka yi mata a baya.

Alhaji Kabiru Dauda dan majalisa Mai wakiltar Gada ta gabas ya sanar da matsayar da kwamitin lafiya da yake jagoranta suka cimma a zaman da suka yi da dan kwangilar da ke gina asibitin zamani dake garin Binji da shugaban asibitin kashi dake Wamakko.

Shugaban ya sanarwa manema labarai cewa sun gayyaci shugabannin ne bayan da suka fahimci akwai saba doka a lokacin da suka ziyarci wuraren.

Kabiru Dauda ya bayyana bacin ransa kan yanda suka tura katin gayyata har sau biyu ga kwamishiniyar amma ba ta ce komai ba a rubuce, haka ba ta turo kowa ba.

"A matsayinmu 'yan majalisar dokoki za mu yi tsayin daka don tabbatar da mutane sun samu abin da yakamata mu kuma kare gwamnati.

"Kin martaba gayyatar mu sabawa aiyukkan majalisa ne  da kin  bin doka, kan haka majalisa ta umarci Kwamishina ta bayyana a majalisa ranar Talata mai zuwa  da karfe 12 na rana, ba a sauraren kowane uzuri na kin halarta.

Dauda ya ce kwamiti bai gamsu da aikin asibitin zamani da ake gudanarwa a karamar hukumar Binji  in aka yi la'akari da aikin da ake yi na asibiti a Tambuwal kuma dukan 'yan kwangilar sun karbi kaso 30 na aiki.

Ya umarci dan kwangila ya koma  ya gyara aikinsa, amma dan  majalisar bai yi magana kan asibitin Sabon Birni wadda duka tare aka bayar da aikin kuma ita ma dan kwangila ya watsar da aikin.

A Wamakko kwamitin lafiya ya aminta zai gudanar da bincike don sanin dalilin bacewar muhimman kayan kiyon lafiya na asibitin.