Red Cross Da Ma'aikatar Jinkai Ta Kasa Sun Raba Kayan Tallafi Ga Mutanen Da Amabaliyar Ruwa  Ta Shafa a Sakkwato

Ambaliyar da ta faru a shekarar da ta gabata ta 2020 an rabawa mutanen kayan abinci da suka hada da buhun shinkafa 100 da wake 100 da gero 100 da kuma buhun masara 100 hadi da man ja da conturola dari-dari. An yi rabon kayan ne a gaban Sakatare na kasa Abubakar Kahende da Sakataren Jiha Shehu Dake da Daraktan lafiya dana kulawa da Annoba da sauran ma'aikatan Red Cross dukansu sun nuna gamsuwarsu ga yanda aka yi rabon ganin wadanda suka amfana da tallafin sun yi fariciki da wannan hobbasar.

Red Cross Da Ma'aikatar Jinkai Ta Kasa Sun Raba Kayan Tallafi Ga Mutanen Da Amabaliyar Ruwa  Ta Shafa a Sakkwato
Kayan Tallafin

 

Kungiyar bayar da agajin gaggawa ta Red Cross da ma'aikatar jinkai ta kasa tare da hadin guiwar kungiyar hadin kai ta Afirika waton ECOWAS sun raba kayan tallafi ga mutanen da Ambaliyar ruwa ta shafa a garuruwan Margai da Girkau dake cikin karamar hukumar Kebbe a jihar Sakkwato.

Ambaliyar da ta faru a shekarar da ta gabata ta 2020 an rabawa mutanen kayan abinci da suka hada da buhun shinkafa 100 da wake 100 da gero 100 da kuma buhun masara 100 hadi da man ja da conturola dari-dari.

An yi rabon kayan ne a gaban Sakatare na kasa Abubakar Kahende da Sakataren Jiha Shehu Dake da Daraktan lafiya dana kulawa da Annoba da sauran ma'aikatan Red Cross dukansu sun nuna gamsuwarsu ga yanda aka yi rabon ganin wadanda suka amfana da tallafin sun yi fariciki da wannan hobbasar.
Haka ma an raba masu kayan amfani da suka hada da takalma silifas da bokiti da tawul da takardar goge kazanta da man goge baki da buroshi da kofuna da zanen rufa.
Sakataren amadadin shugabanni ya yi kira ga wadan da suka samu wannan tallafi su yi amfani da shi ta hanyar da ta dace kar su walaknta abin da aka ba su ko su sayar.
Ya ce amfani da kayan shi ne zai nuna sun gode da karamcin da aka yi masu, hakan zai baiwa hukumomi kwarin guiwa a baiwa wasu mabukata a wasu garuruwa a nan gaba.

Daga Muhamma M. Nasir