Hussain Ibrahim, Gusau.
Mataimakin masu saida magunguna na Kasa ,kuma Shugaban Ma'aikata na jihar Zamfara, Kwamaret Sani Haliru,ya bayyana cewa,masu saida magunguna na da rawar da za su taka wajan dakile saida haramtatun kwayoyi masu sanya maye a fadin Kasar nan.
Kwamaret Sani Haliru ya bayyana haka ne,a Kasidar da ya gabatar a Taron fadakarwa akan illar amfani da masaukin baki masu zaman kansu da hukumar N D L A ta shirya a Gusau babban birnin jihar Zamfara.
A Kasidar ta shi Kwamaret Sani Haliru ya bayyana cewa, Masu sai da magunguna na iyaka kokarin su wajan ganin sun kauce wajan saida milyagun kwayoyi masu lallata tarbiyar al'umma. 'Kuma Kungiyar mu na iyaka kokarinta na ganin ta fadakar da mambobinta wajan ganin sun bi doka wajan tsaftace sana'ar su ta saida magunguna', inji Kwamaret Sani Haliru.
Kwamaret Sani Haliru ya jinjinawa hukumar yaki da fataucin Miyagun kwaya akan shirya bita da tayi ga masu Hotal dan gargadin su akan masu amfani da Hotal dan saida Miyagun kwaya da Shaye-Shaye.
A karshen yayi kira ga mambobin su da suji tsoran Allah wajan sana'ar su ta saida magunguna ,wajan saida masu kyau kuma a guji saida Miyagun kwaya dan baisa mutum arziki.
Kuma Suma masu Hotal ya kamata su kula wajan ganin sun tsaftace bakin su ,da bincike abubuwan da suke aiwatarwa a dakunan kwanan su.idan sun ga bakin da ba su gamsu da su ba koma suna zarginsu da wani abu na aibu su gaggauta sanar da hukuma dan daukar.ataki akai.