Home Daga Marubutanmu RAUNIN RAYUWA: Fita Ta Takwas

RAUNIN RAYUWA: Fita Ta Takwas

16
0

Page:  8

A can tsakar gida Sadiya ce ta bi bayan Surayyar da kallo a lokacin da take wucewar tana riƙe haɓa sai da ta tabbatar ta shige ta dawo da dubanta ga fuskokin mutanen wajen tana faɗar “Ikon Allah na kwance ya faɗi! Ita kuma wannan yau me yake damunta ne mama?”

“Me kika gani ne?” Maman ta tambaya.

“To ai na gan ta ne ba a yadda na saba ganin ta ba, duk lokacin da za mu zo cike da fara’a take tarbarmu har ta ɗauki Airah ta yi mata wasa, amma kin ga yau mu kanmu ma kallon hadarin kaji muka samu ballantana ‘ya’yan.”

Mustapha ya amshe zancen da fadar “Gaskiya ni ma na ga sauyi a tare da ita, ƙila akwai abun da ke damunta.”

A’ishatu ta yi wuf ta ce “Ba fa wani abu da ke damunta kawai baƙin halin ne yau ya motsa.” 

“Kai! Ai ko ba za ki ce ‘ya’ya Surayyah tana da baƙin hali ba, wannan sai dai ke ai…” Sadiya ta mayar mata.

Sai a lokacin maman ta buɗi baki ta ce “Wai fa kunama ce ta harbe ta jiya da dare shi ne yau take ta wani logaye-logaye tamkar mara lakka.”

Sadiya, Uwani da Mustapha suka zazzaro ido Mustaphan ya ce “Subhanallahi! Kunama fa mama? Shi ne kuma kike nuna kamar ba wani abu ba ne? Ko kin manta dafi yana iya kisa kai tsaye?”

Mama ta kawar da kai gefe tana yunƙurin miƙewa tsaye “Ban da ma abinku na yaran zamani ai ya ci ta yi juriya fiye da haka, ita fa uwa ce a gaba haka za a yi haihuwar? Kai dai Allah ya sauwaƙe mata.”

Ko da ta ƙarasa zancen ta gama miƙewa ta yi hanyar ɗaki.

Tsantsar tausayi ya bayyana a fuskar Sadiya ta ce “Allah sarki yayata! Yanzu na ji dalilin sauyinki, Allah ya taƙaita wahala, bari na shiga ciki na duba ta.” Ita ma ta miƙe rungume da ‘yarta Airah mai shekara ɗaya da rabi ta bi bayan mama zuwa ciki. 

Ko motsawa Uwani ba ta yi daga gun ba sai dai ta ce “Allah ya yaye ya kiyaye gaba.” Suka ci gaba da hirarsu ita da A’ishatu, Mustapha ne ya wurga musu harara “Ku ba za ku tashi ku je ku gaida ita ba ne? Ko kun fi ƙarfin hakan ne?”

A’ishatu ta turo baki gaba “Kai yaya Musty ni dai na ga tare za mu wuni da ita a gidan nan sannun nan zan yi ta ko ba yanzu ba.”

Ita ko Uwani sai ta ce da shi “Ɗakin ya yi zafi da yawa yaya Musty idan ta fito zan gaishe ta kafin na tafi.”

Bai tsaya bi takan ƙannan nasa ba don ya ga alamar kansu na rawa sai kawai ya girgiza kai a can ƙasan maƙoshi ya ce “Allah ya kyauta.” Shi ma ya bar musu gun ya je ciki don duba tan.

A can cikin ɗakin mama ce ta fara isa ta tsaya a gefen kan Surayyar tana faɗar “Sannu Surayyah, ya jikin dai?” Ta amsa da “Alhamdullillah mama.”

“Me likitan ya ce ne?”

“Haka ya ce da sauƙi, amma sai na kula da shan magani da kyau don wurin zai iya harbuwa da ƙwayoyin cutar infection, Kuma ya cire ɗaurin da Baffa ya yi mini a cewarsa hakan zai hana jini gudanawa da kyau kuma ya riƙe jijiyoyin ƙafar.” Daidai nan Sadiya ta shigo ɗakin da sallamarta, mama ta amsa, ta ƙaraso ta zauna a ƙasan kujerar da Surayyan ke kai daidai lokacin da mama ke faɗar “Allah ya sauwaƙe, ki yi haƙuri Surayyah ban san abin ya yi rauni haka ba na yi ta saka ki aiki.” Idan ka kalli fuskarta a daidai lokacin za ka tabbatar tana tausayin ‘yar tata har sai ka yi mamakin yadda take nuna kamar ba ta tausayinta a zahiri amma idan ka yi la’akari da azanci da Hausawa kan ce kaza tana taka ‘ya’yanta ne ba don ba ta son su ba sai ka yi mata uzuri.

Girgiza kai ta yi alamar ba komai ya wuce. “Sannu yayata, ashe abin da ya faru kenan? Allah ya ba ki lafiya ya tsare gaba.”

“Amin na gode.” Ta faɗa a taƙaice tana lumshe ido saboda baccin da yake ɗibar ta sai kuma ta tuna ashe ba ta samu yin sallar la’asar ba a asibitin, ta fara ƙoƙarin tashi zaune Sadiya ta ce “Anyah ma kin ci abincin rana kuwa yaya?”

Kafin wani ya yi ƙoƙarin ba ta amsa ta sake faɗar “Kai! Na tuna ba komai yake yi wa mara lafiya daɗi ba, bari na ɗauko miki fruit Salad ɗin da na zo da shi, musamman na yi order shi saboda mama tana so…” Ta mayar da duban ta ga maman, “ina kika ajiye na ɗauko mata?”

Maman ta kwatanta mata inda ta ɓoye shi wannan karon ko mita ba ta yi ba ta ce a ɗauko duka a ba wa Surayyar ta sha wanda zai ishe ta ta ba su ragowar kafin Aishatu cinye-duk ta gani. 

“Na gode Sadynmu bari na yi sallah ko?” Ta faɗa da murmushi a fuskarta daidai za ta fita ƙofa kenan suka ci karo da yaya Mustapha shi ma ya gaishe ta ya juya ya fice daga gidan gaba ɗaya. Ko da ta fita wajen ma ba ta kalli sashin da ‘yan’uwan nata biyu suke ba ta je ta yi abin da ya fito da ita ta koma ɗaki ta tada sallah da ta gama ne ta kwanta a ƙasan carpet ta ɗora filo ta sha baccinta, duk da kuwa ta sha ji ana faɗar baccin bayan la’asar ba shi da kyau wai yana gadar da talauci da baƙin rai, amma nata ai na lalura ne ba yadda ta iya.

Bayan sallar isha’i su Sadiya suka koma ɗakin mazajensu, su kuma su Surayyah suka fara shirin tafiya gidajen kwanansu. Sai da ta sha maganinta na dare ta ɗebi waɗan da za ta yi amfani da su da safe ta zuba a leda. Tana cikin shirin ne mama ta shigo ɗakin ta kalle ta da tausayawa. “Anyah kuwa yau za ki iya tafiya babban gida a ƙafa, ko dai na nemo wanda zai kai ki?”

“Kar ki damu mama, jikin ai da sauƙi zan lallaɓa.” A’ishatu ta kalle su kawai takaici ya hana ta yin magana, wai don ɗan wannan ciwon ne ake wani lelenta kamar wacce aka ce musu yau za ta mutu, ba dai ta ce komai ba ta ƙume haushinta ta ci gaba da sabgogin gabanta.

Mama ce ta ƙara cewa “A’ah! Ban yarda ki fama ciwon ba, jira idan yayanku Mustapha ya shigo yin sallama zan sa ya sauke ki a can. Ni da ba don ba don ba ma yau ba dalilin da za ki je can gidan don sun matuƙar ban haushi, a ce a gabansu abin nan ya faru amma duk yawan zuri’ar gidan a rasa wanda za a turo ya duba lafiyarki? Haka ake rayuwar?”

Surayyah dai ba ta ce komai ba don kuwa maganar maman abar dubawa ce, duk da dai tasan bayan faruwar abin ba ta koma ciki ta sanar ba amma tana da tabbacin labari ya riske su da safe don kuwa ba ta yadda irin wannan abu zai faru a cikin gidan ya haura awanni goma ba tare da labarin ya kewaye kafatarin gidan ba. Ta ji haushin yadda suka yi halin ko in kula da ita, sai dai ta ji a ran ta cewa ba komai ciwo ne ya san ƙofar gidan kowa.

Yadda mama ta faɗa hakan ce ta faru Musty ne ya sauke ta da misalin ƙarfe tara da rabi ta shiga gidan da sallama, yau ba ta tsaya leƙa ƙofofi tana gaishe su ba kamar yadda ta saba duk sanda ta shigo gidan, kai tsaye ta wuce can ƙuryar gida ta shige ɗakin kakarsu mahaifiyar babansu Hajiya Innare. Sa’in da ta shigo ba kowa a tsakar gidan kasantuwar akwai wutar lantarki duka yaran sun rar-rabu a ɗakunan matan gidan suna kallon tv ba ka iya jiyo komai a tsakar gidan sai hayaniyarsu.

Can da misalin ƙarfe goma da rabi aka ɗauke wutar dalilin da ya saka mazauna gidan suka fara fito da shimfiɗunsu waje, ko da Surayyah ta leƙo ta tarar Minal ta canzawa katifar muhalli daga inda ta saba shimfiɗa musu, yau sai ta saka a daf da ƙofar mamanta. Ta ji a ranta akwai wata a ƙasa, amma duk da haka da wankakkiyar zuciya ta ɗauki filonta ta nufi can saboda ta kuɗurce a ranta su ahali ne duk girman rikicin da zai shiga tsakaninsu ba zai taɓa sauya wannan alaƙar jinin da suke da ita ba, don haka ko za ta yi fushi ba za ta yi gaba ba.

Sai dai tana ɗora filonta a kai Minal ta yi wancakali da shi a gefe tana faɗar “Yau dai abi wani sarkin ba ni ba…”

BANGAREN HALISA

Kallon cikin idanunta malamin ya yi kafin ya yi musu umarnin ficewa daga ajinsa, sum-sum suka ja jiki suka fice tamkar munafukai, shi kuma ya juya ya ci gaba da aikinsa, wannan hukuncin da ya yi musu ya sa sauran ɗaliban suka shiga taitayinsu ajin ya yi tsit kamar ba rayayyu a ciki.

A can ƙofar ajin Halima ta kalli Halisa cikin tuhuma, “Kin ga abin da nake gudu ko Apsara? Sai da na ce miki mu daina amma ga shi nan ai kin janyo an koro mu waje, yanzu duk wanda ya ganmu a nan ya san ba shakka babban laifi muka aikata.”

Ta yi zancen kamar za ta fashe da kuka.

Dariya Halisa ta yi cikin rashin kula ta ja hannun Halima suka ɗan yi taku uku sa’annan suka zauna kan dandamalin ƙofar ajin nasu tana faɗar “Don Allah manta da shi, ni ai hakan ya yi mini da ma wa ke gane karatunsa? Ban da tallar surar jiki me yake zuwa yi a ajin? Habah! kina dai gani mutumin nan kullum sai dai ya yi ta haɗa lissafinsa a bango shi kaɗai yana gogewa mu sai dai ya bar mu da kwafi, wannan ai ma kansa kawai yake koyarwa.”

Wannan karon ita ma Haliman dariya ta bushe da ita sai kuma ta tofa nata albarkacin bakin. “Wallahi kuwa, shi fa ɗauka yake kowa ma ya riga da ya san abin da shi ya sani.”

Suka tafa su biyu suna ɓingirewa da dariya daga ciki uncle Markel ya leƙo yana faɗar “You are disturbing us, come in you idiots!” 

Shan jinin jikinsu suka yi ganin yadda yake muzurai ga shi riƙe da dorina a hannunsa, don kuwa duk taɓarar Halisa tana tsoron abin da zai taɓa lafiyarta. Tashi suka yi suka nufi ƙofar sai kuma aka rasa wacce za ta fara shiga suka tsaya suna dibibita. Wata tsawar ya sake doka musu ce ta sa hanjin cikin Halisa suka kaɗa har ba ta san lokacin da ta afka cikin ajin ba, ai kuwa faɗawarta ke da wuya ta ji saukar lafiyayyiyar bulala mai daɗi a gadon bayanta. Wani uban tsalle ta daka tana sakin shagwaɓaɓɓiyar ƙara “Ahhh!” Kafin ta dire ƙafafuwanta ƙasa ya shauɗa mata biyu masu kyau a tare. Ganin haka ya sa Halima ta ƙame a ƙofa ta kasa ƙarasowa, har can ya same ta ya yi mata nata hukuncin sannan ya yi musu umurnin komawa mazauninsu tare da kashedi na ƙarshe.

Tun da suka zauna ba wacce ta sake ƙwaƙwaran motsi har ya bar ajin. Ko bayan ya fita ma ba su ƙarasa kitson ba saboda masifar tsoro irin na Halima ta gwammace ta bari a tashi daga makaranta sannan su yi zaman ɓata lokacin yin kitson. Halisa ba ta ce da ita komai ba ta ƙume daɗinta sai da aka tashin Haliman ta roƙi ta ƙarasa mata aikin da ta fara, a nan ita kuma ta daka tsalle tara ba ta taɓa ƙasa ba ta ce sam ba ta san zancen ba idan ma har za ta ƙarasa to sai dai gobe don ba za ta yarda abokanan tafiyarta su yi gaba ba. 

Wannan garaɓasar da suke kwasa ta rahusar abin hawa da kuma romon neman magana da take yi a hanya ba za ta so ya wuce ta ba. Bisa ga tilas Haliman ta ɗaure rabin gashin kanta da ribborn don kuwa sanannen abu ne tun da Halisa ta ce ba za ta ƙarasa mata ba sai gobe to ba za ta sauya ba, ta naƙalci halayenta sosai ta kuma fuskanci kamar fushi ta yi da ita saboda lokacin da ta nemi ta zo su ƙara bayan fitar uncle Markel tsoro ya hana ta amincewa.

Ranar ma haka suka juya gida cikin irin yanayin cunkushewa da suka saba yi a cikin abin hawa, sai dai a ranar tsamin jiki da take fama da shi ya hana mata dagewa  ta yi tsokana duk da haka ta ɗan taɓa halin sama-sama. Suna isa gida kafin su shiga ciki ta tarar da motar Hayat ajiye a  ɗan nesa kaɗan da ƙofar gidansu,  ba sai an faɗa mata ba ta san wurinta ya zo. 

Duk da ba ta wani kula shi sosai amma ba ta san dalilin da ya sa ta ji wani sanyi yana  ratsa mata zuciya ba sai dai duk da hakan sai ta basar ta yi kamar ba ta san da wanzuwar motar a wajen ba duk da tana kyautata zaton yana zaune a cikin motar don ratsewa rana haka ta ɗauke kai ta ratse ta gefen motar saitin mazaunin direba inda take da tabbacin in dai ta gifta ta gun zai gan ta. Ba ta kalli ɓangaren ba don kada ma ya saka ran ta gan shi. 

Ai kuwa kwalliya ta biya kuɗin sabulu saboda tana bada baya ya hango ta kuma ya gane ta duk kuwa da cewa iya bayanta ya gani, masu iya magana kan ce ko cikin duhu talaka ya san nashi. Da iya tafiyarta kawai zai tantance ta a cikin mata ɗari, so ai ba ƙarya ba ne. 

Hanzarin buɗe motar ya yi ya fito yana ƙwala mata kira “Apsara baby! Apsara baby!!” Yi ta yi kamar ba ta gan shi ba ta ci gaba da kusantar ƙofar gidansu. Cikin gudu-gudu sauri-sauri ya sha gaban ta yana watsa mata mayataccen kallon sa da ya saba yi mata yana faɗar “Au! Shi ne kika yi kamar ba ki gan ni ba za ki shige? Na kira kuma kika ƙi tsaya wa baby?”

“Ni ka daina ce mini baby ni ba ‘yar tsana ba ce.” Ta yi zancen a shagwaɓe tana mummurguɗa ƙaramin bakinta.

Hannunwansa ya rungume a gadon bayansa har a lokacin bai ɗauke idonsa a kanta ba ya ce “To na ji bab….” Sai dai tun bai ƙarasa ba ya toshe bakinsa da tafin hannu kafin ya mayar da hannun kan kunnuwansa ya kama ya  ɗan sunkuyar da kai kaɗan yana kallon fuskarta da yadda ta zumɓure baki da kaɗa kai alamar ya yi kyau, “Afwan na tuna Apsara ba zan ƙara ba. Yanzu dai ya za a yi gani na zo hira.”

“Tab! Hira da wannan uwar ranar? To ni dai yau a gajiye nake sosai, ka ga shigewa ta.” 

Ta sa kai ta ci gaba da tafiya tana fatan ya biyo ta sai dai bai yi hakan ba kawai dai ta jiyo muryarsa a sama yana faɗar “Ba damuwa Apsara wutar kyau, kin kai a jira ki. Zan je gidansu Mahmud abokina na nan bayanku bayan mintuna arba’in zan dawo, na san dai sun ishe ki hutu ko?” Ba ta ce komai ba sai canza salon tafiyarta ta yi zuwa karairaya ta shige. 

Ummu Intisar ce

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here