Home Daga Marubutanmu RAUNIN RAYUWA: Fita Ta Bakwai

RAUNIN RAYUWA: Fita Ta Bakwai

25
0

PAGE 7

ƁANGAREN SURAYYAH

Kamar kububuwa ta faɗa ɗakin ta fisge farantin ƙosan da iya ƙarfinta tana faɗar “Ke kin isa? Wane irin rashin hankali ne wannan na ajiye abincina ki ɗauka mini?”

Cikin gadara Aishatun ta ba ta amsa da “Tashi ne ba zan iya yi ba shi ya sa na ɗauka, da alama ma kin gama zaɓe masu kyaun, shi ya sa ba ki jira an raba ba saboda kin tasar wa zalunci.” Ta ƙarasa zancen da murya ƙasa-ƙasa tana kalato ƙosan da suka zube a ƙasa. Cikin zafin rai da zafin hannu Surayyah ta ɗima mata dundu a gadon baya tana huci da faɗar “Don kin ga ba na magana shi ya sa duk rashin kunyar da kika yaɓo kike zubewa a kaina ko? Wato ga juji mai daɗin zuba shara ko?”

“Mamaa!  Kina ganin ta ko mama?” A’ishatu ta ɗago da guntuwar ƙwalla a idanunta tana kallon mama cikin ido tana jira ta ga matakin da za ta ɗauka. Maman ta miƙe daga kan kujerar da take tana nufo gun a lokacin da take faɗar “Ba ki da hannu ne? Idan kina da hannu maza ki rama dukan da ta yi miki, ai idan tsoho bai ji kunyar hawan jaki ba jakin ba ya kunyar tiƙa shi da ƙasa.”

Ta yi maganar cikin rashin kula da abin da zai biyo baya, daidai lokacin ta iso gun ta karɓi farantin a hannun A’ishatu tana faɗar “Kawo na ƙaro miki ƙosan ‘yata.”

Sororo Surayyah ta tsaya tana kallon mama da sakakken baki, shin wannan wane irin hukunci ne? Adalci ne hakan ko ƙiyayya?

Kafin ta gama zancen zucin ta ci saukar dundu a gadon baya, ba ta buƙatar sai ta waiga ta san aikin Aishatu ne bayan karɓar umurni daga mahaifiyarsu, ba ta san lokacin da ƙwalla ta sirnano mata daga ido ba, ba wai zafin dukan da Aishatu ta yi mata ba ne  ya saka ta kuka face dukan zuciyarta da mama ta yi da wannan hukuncin. ‘Me ya sa ne har kullum ita idan ‘ya’yanta suna faɗa take goyon bayan ƙarami a kan babba?’

Ita a iya tunaninta da nazari kan doron hankali ba ta hango dacewar hakan ba, ta fi hango dacewar zancen da malaminsu na islamiyya ya faɗa musu cewa “Bai kamata uwa ta yi wa babba hukunci a gaban ƙannensa ba, ko da shi ne mara gaskiya to idan za ta yi faɗan ta fi karkatar da tsagin laifin ga ƙarami. Sai bayan idanunsa sai ta kira babban ta yi masa faɗan dabam tare da nusar da shi gaskiya domin ya gyara a gaba. Ta haka ne kaɗai ƙaramin zai ci gaba da ganin ƙima da girman yayansa kuma ya taso mai matuƙar ladabi da taka-tsantsan.”

To sai dai ita a gidansu kullum saɓanin hakan ke faruwa yau har ga inda ta kai su, an saka ƙaramar ƙanwarta ta uku da a ƙalla ta ba ta shekaru 9 lafiyayyu ta sa hannu ta dake ta, a gaba kenan me zai faru?  

Da wannan tunanin ta wuce uwar ɗaka tana hawayen baƙinciki ta sako tufafi, atamfa koriya ɗinkin riga da siket sai hula baƙa, a falo ta wuce A’ishatu tana ci gaba da karyawa da alamu maman ta ƙaro mata ƙosan don ta gan shi a cike, kallon gadara Aishatun ta aiko mata tana ci gaba da yin mamur-mamur da baki.

Ba ta kula ta ba ta yi waje ta nemi guntuwar tabarma ta shimfiɗa a gefe ta rakaɓe tana sauraren zazzaɓin jikinta. A wajen ta tarar da mama ta dandale kan dandaryar siminti da ƙaton farantin silver a gabanta tana faman kashi. 

Ba ta ce ƙala ba sai kwanciya da ta yi ta rufe idanunta zuciyarta na yi mata tariyar lokutan baya musamman lokacin da suke zuba soyayya da Amir bayan an yi masa nemanta.

 Can ta hasko wani daren juma’a da misalin ƙarfe bakwai da rabi na dare Amir ya kirawo ta a waya kan cewa ga shi a ƙofar gida. A shirye take tsaf ta fito za ta tafi mama ta tare ta a tsakar gida, “Ke ina kike sauri za ki? Haba! Ba ko ɗan jan ajin nan na mata? Su fa maza ba a rawar ƙafa da su, yana da kyau ki koya masa jira ko don gaba tun za a je ake shiri ba sai andawo ba. “

Bisa ga tilas ta tsaya gun sai bayan cikar mintuna uku maman ta yi mata umurnin fita. Ko da ta fito ta same shi ya fara hasala sai dai ganin ta da ya yi ya sa ya nemi ɓacin ran ya rasa, gaisawa suka yi a gurguje ya miƙa mata manyan ledoji guda biyu da ya shaƙo su cike da kayan ciye-ciye ya ce da ita “Wannan naki ne baby, kin san ba zan iya ci ni kaɗai ba.” 

Ƙayataccen murmushi ta sakar masa ta karɓa tana faɗar “Ni ɗin ma ai haka ne a ɓangarena, na gode Allah ƙara buɗi.” Ya amsa da amin sannan ya ɗale babur ɗinsa yana faɗar “Ni zan koma akwai inda za ni ne cikin daren nan.”

“Ok, bye ka kula da kanka.”

Cikin gidan ta shiga niƙi-niƙi da kaya mama ce ta fara tarbonta tana faɗar “Toh! Ikon Allah me muka samu haka?”

“Ga su nan dai mama, sai mun buɗe za mu gani.” A’ishatu da zumuɗi ta wuce kitchen ta ɗauko farantin ta zo ta ajiye a gaban Surayyah tana faɗar “Ko ma miye ba zai wuce na ci ba antyna zazzage shi a nan.”

Kaza ce danƙwaleliya irin wacce ake yi wa haɗin Irish a cikinta a ɗinke, sai cakes kala-kala a cikin wata leda za su kai kala shida kama daga kan slice cake, sponge cake, orange cake chocolate cake duka. A ɗayar ledar kuma kayan sanyi ne kala uku, exotic babban kwali, hollandia da tiƙeƙiyar robar yogurt.

Nan ta bar wa mama kayan sai da suka ɗibi wanda ya yi musu ita da A’ishatu sannan aka ba ta saura ta shiga da shi,  har a lokacin tana hasko sa’in da mama ta cika baki da kaza tana faɗar “Allah ya yi miki albarka Surayyata, Allah ya nuna mini aurenki da Amir, ya nunan ranar da za ki aiko mini abincin alfarma daga ɗakinki.”

Ta zo daidai nan a tunaninta ta ji an zunguri ƙafarta da ƙarfi, mama ce tsaye a kanta tana miƙo mata wata ‘yar ƙaramar roba da ta zuba mata nata kason a ciki, sai kokon a babban kofin roba tana faɗar “Ga naki kason, shi ma idan ba za ki ci ba ba matsala Dije dai ta gama nata aikin.” 

Ba ta ce komai ba ta karɓi abincin a raine ta ajiye a gabanta da kamar ta yi zuciya ta ƙi ci, amma ba yadda ta iya masu azanci sun ce tambarin talaka cikinsa don haka ba ta da zaɓin da ya fi ta ci abincin ko don kawar da yunwar cikinta.

Haka ta ci abincin tana kukan zuci bayan ta kammala a nan wurin ta kirifce tana sauraren zogin ƙafarta da wurin ciwon ya fara kumbura. Sai can bayan azahar baba ya dawo gidan ya miƙa mata kuɗi dubu uku ya ce ta je can gidan gandunsu ta nemo wacce za ta raka ta asibitin don duba lafiyarta. Tana karɓar kuɗin kamar mai jira ta miƙe ta ja hijabinta bayan ta yi masa godiya ta fita, sai dai ba ta ɗauki kasadar komawa can gidan ba don haka ta nufin gidansu aminiyarta Maryam da yake kusa da nasu don gida biyar ne a tsakaninsu.

 Maryam ɗin ta roƙa don ta raka ta asibitin ita kuma ta nuna mata ta roƙi inna Huwaila (kishiyar mamanta) da take a hannunta ko za ta bar ta su je tare. Da son samu ne ba ma za ta kula inna Huwailar ba saboda yadda take wahalar mata da ƙawa a gidan, amma da ta tuna da mamanta da ta haife ta ma kusan irin wannan riƙon take yi mata sai ta ji ta rage jin haushin Inna Huwailar, ko ba komai ma dai dole ne ita ce za ta bada umurnin fitar saboda matsayin uwa da take kai don haka cikin sanyin jiki ta ƙarasa ƙofar innan tana doka sallama. 

Daga ciki innan ta ce “Waye ne? Shigo ciki.” Ta yi kamar yadda ta umurce ta, ta tarar da ita zaune a ƙasan gado tana ɗaura garin kukar da take sayarwa a leda ta duƙursa a gabanta. “Ina wuni inna? Ya kasuwar?”
Kallo ɗaya innan ta yi mata ta ɗauke ido tana ci gaba da aikin gabanta tare da amsa mata ciki-ciki. “Lafiya qlau.”

Surayyah ta girgiza kai cikin ranta ta ce ‘Hali baran azaliya.’ A zahiri kuwa cewa ta yi “Um, da ma Inna abbanmu ne ya ce na zo na roƙe ki don Allah ki ba ni aron Maryam ta raka ni asibiti a duba ni kunama ce ta harbe ni jiya da dare.”

Tana zuwa nan a zancenta ta yi shiru tana jiran ta jin amsar da innan za ta ba ta, sai dai a haka sakanni masu yawa suka shuɗe ba ta ji ta ce da ita komai ba kamar ma ta manta da wanzuwarta a gun, har ta buɗi baki za ta sake yin magana sai ta ji ta ce “Tun da kin ce abbanku ne ya roƙa ba komai kin ci albarkacinsa je ki ki ce ta shirya yanzu ku tafi, amma kar ku kai magariba.  Akwai ayuka da yawa da suke jiran ta idan ke ba ki da su.”

Ita dai godiya kawai ta yi ta miƙe tana mamakin halin matar da yadda take gadara a cikin maganganunta, ‘wannan da ita ce mahaifiyar Maryam da ƙawancen nan namu ba inda zai je. Wannan izza haka?’ Ta faɗa a ranta.

Ɗakin Maryam ta shiga ta sanar mata yadda suka yi  da hanzari Maryam ta miƙe kamar wacce da ma can a kan ƙaya take ta ajiye tsintsiyar hannunta ta sauya kaya a gurguje suka fito suka tari abin hawa.

A cikin adaidaitar Surayyah ta kalli Maryam cikin tausayawa ta ce “Ƙawata ya muka ji da haƙurin wannan ƙaddara ta zaman gida?”

“Ke dai ki bari kawai ƙawata! Mu dai sai godiyar Allah taskun yau dabam da na gobe. Ke da ma sauƙi tun da a gaban mahaifiyarki kike ko ya ya ne watarana za ki samu sassauci domin ko ita za ta yi miki don ki zuciya ki yi aure to ba za ta bari wasu su zage ki ko su yi miki isgili a gaban idonta ba, amma ni fa?” Ta mayar tana kallon Surayyan.

 Surayyar ta yi murmushin yaƙe ta kaɗa kai gefe. “To da dama-dama ciwon ciki hanji a fili, amma gaskiya na fara ƙosawa da wannan rayuwar, wani sa’in haka kurum zuciyata ke raya mini idan na samu wanda zai aure ni koma waye kawai na amince don na matsa na bar wannan rayuwar…”

Maryam ta tari numfashinta da faɗar “Akul ɗinki da wannan mummunan tunani ƙawata! Mu dai ƙara haƙuri Allah bai manta da mu ba yana sane da halin da muke ciki, ba mamaki akwai alkhairan da ya tanadar mana a cikin jinkirinmu. Sau da dama jinkiri alkhairi yake zamewa ma’abocinsa, sau tari a kan hana ka abin da kake so don sauya maka da mafificin shi amma za a iya ba ka wanda kake so ya zama ba alheri a ciki.”

“To Allah ya zaɓa mana ma fi alheri.” Ta faɗa tana shafa wayar Android da ke hannunta kafin can ta ce “Af! Ni ko Maryam ina mutumina Sajid na daina jin labarinsa. Tun lokacin da ya nemi ki ba shi da ma ya turo iyayensa ban sake jin batun a kansa ba, ya kuka ƙarge kuwa?”

Murmushi mai ciwo Maryam ta yi, yadda yanayin fuskarta ya sauya kaɗai ya isa ya tabbatar wa da duk mai kallonta tana cikin alhini da ciwon rai game da zancen da aka ɗauko. Ta ce “Hmmm! Ki bari kawai ƙawata, ba ma na son tunawa.”

Ta ja dogon tsaki daidai sa’in da Surayyar ke tambayarta “Me kuma ya faru?”

“Ai in faɗa miki ni dai ba abin da na san na yi wa bawan Allahn nan haka kurum na neme shi na rasa abun kamar da jifa. Da na ga ya daina kirana, ya daina zuwa ya yanke duk wata alaƙa da ke tsakaninmu hatta a social media, sai kawai na yanke hukuncin kiran shi na ji ba’asi kin san wai an ce da rashin kira karen Bebe ya ɓata, to kin ko san ko me ya faɗa mini bayan ya ɗaga kiran da ƙyar?”

Wannan karon Surayyah ba ta samu damar ba da amsa ba sai girgiza kai da ta yi alamun ba ta sani ba.

Maryam ta ɗora da faɗar “Ce mini ya yi wai na yi haƙuri don Allah, zancen auren nan ya janye kuma shi har ga Allah ba abin da na yi masa kawai dai ya wayi gari ne ya ji ra’ayinsa ya sauya a kaina. A labarin da yake ba ni ma a lokacin an yi engage ɗinsa da wata don haka yana mai yi mini fatan alheri da fatan Allah ya zaɓa mini miji nagari wanda ya fi shi.”

Ta ɗan tsahirta ta sauke numfashi kafin ta ɗora da faɗar “Tsabar kaɗuwa ban iya ƙara ce masa komai ba na kashe waya na yasu a nan inda nake, ban san lokacin da na fara hawaye ba. In taƙaice miki saboda baƙinciki a ranar ban iya bacci ba. Na yi ta tunanin ko wani zunubin ne nake aikatawa ake yi mini hukunci da irin waɗannan jarabawoyin rayuwar.”

Dogon numfashi Surayyah ta ja ta sauke cikin tausayawa ƙawar tata ta ce “Kai lallai Sajid ya cika mayaudari mai wasa da zuciya, amma ba komai Allah ya zaɓa miki wanda ya fi shi alheri. Mahaƙurci mawadaci watarana mu ma za mu dara kamar sauran mata in sha Allahu.”

Ta amsa da Amin, haka suka ci gaba da tattauna batutuwan da suka shafi ƙalubalen rayuwar da suke fuskanta har zuwa lokacin da mai adaidaitar ya sauke su a gate ɗin general hospital Rigasa duka tafiyar da suka yi ba ta haura mintuna sha biyu ba a haka ma don sun ci karo da cinkoson ababen hawa a hanya.  

Har a lokacin akwai zafin zazzaɓin a jikinta kawai ƙarfin hali take yi, wurin da harbin yake ya ƙara kumbura sosai wanda take kyautatawa zaton har da tafiyar ƙafa da ta yi da kuma wahalar zama gaban murhu da wannan zafin ne ya ƙara tsamarin jinyar.

Ta zaro kuɗi daga aljihunta ta miƙa masa ya ba ta chanji suka shige ciki tana jan ƙafa don ya ajiye su ne a daidai hannunsu ba zancen yin tsallaken titi.

Sun fi awa biyu kafin samun damar ganin likita bayan sun yanki kati, ta yi wa likitar duk bayanin da ya dace ta rubuta mata magungunan pain reliever da anti biotics saboda bada kariya daga hatsarin kamuwa da ƙananun ƙwayoyin cuta suka dawo gida. Sai da ta raka Maryam har gida ta ƙara yi wa Inna Huwaila godiya sa’annan ta dawo ta shiga gidansu duk a gajiye lokacin ƙarfe biyar saura kwata na yamma, ta samu gidan nasu da baƙi Sadiya ƙanwarta mai bi mata da Uwani wacce take bin Sadiyar ne suka zo ganin gida.

 Ita kuwa lokacin ba ta cikin yanayi mai daɗi, ta zo za ta wuce suna zaune a kan tabarma cikin rumfar ɗaki suna hira da Mama, Aishatu da kuma yaya Mustapha.

 “Ah! Yau baƙi ne da mu a gidan kenan? Sannunku da zuwa.” Ta faɗa a kasalance ba ta zauna a gun ba kawai ta sunkuya ta ɗauki ledar fiyawota ɗaya daga cikin ruwan da ke ajiye cikin roba a tsakiyarsu ta yi wucewar ta cikin ɗaki tana yasuwa a kan kujera tare da buɗe ledar maganin da ke hannunta ta ɓallo kamar yadda likita ya yi mata umurni ta sha sannan ta cire hijabi domin ta sha iska ta kishingiɗa kan doguwar kujera.

Tofah! Ya za a ƙare tsakanin Fatima da mijinta? Za ta yi nasara a kan mummunan kudirinsa ko shi ne zai yi nasara a kanta? Mi ne ne zai zama raunin rayuwarta a gaba?

Surayyah fa, yaushe kaɗɗarar da take bibiyarta za ta sauya mata zuwa kyakkyawa? Ya rayuwa za ta ci gaba da gara mata a gidansu? Shin za ta iya yaƙar raunin rayuwarta ko kuwa raunin ne zai dulmiyar da ita?

Tofah! Ga kuma Halisa (Apsara wutar kyau) shin ɗabi’unta za su cutar da rayuwarta ta gaba? Aina nata raunin Rayuwar yake?

Waɗannan da wasu tambayoyin makamatansu da suke kara-kaina tsakanin zuciya da ƙwaƙwalwarku duka za ku sa mu amsar su a shafin gaba.

Da wannan na kawo ƙarshen free pages Kuma nake cewa mu haɗu da ku a paid group, waɗanda suka biya suna cikin alheri dumu-dumu don ko wannan labarin yanzu ma aka fara ba yi komai ba yanzu ne za a yi, wannan salonsa dabam ne da na ba ya.

Wasa farin girki.

UMMU INTISAR CE

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here