Na
Ruƙayya Ibrahim Lawal ( Ummu Intisar)
Halin paid group ya me na rage jin motsinku kwana biyu meke faruwa? Kusa ni kin motsinku a kusa da sharhinku yana ƙara mini karsashin yin rubutu. Allah ya ci gaba da yi wa rayuwarmu albarka.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
PP 27
BANGAREN SURAYYAH
“Surayyah ni kike faɗawa magana yau?”
Mama Hadiza ta yi furucin cikin matuƙar kaɗuwa da mamaki, domin kuwa duk irin yadda suke yi wa Surayyah abubuwa kala daban-dabam a gidan ba ta taɓa buɗe baki ta mayar mata da martani ba sai yau.
Iyakacinta duk ta yi iya ƙoƙarinta wurin kare kanta da kalamai ko ta mayarwa ƙannen nata martani aa wasu lokutan amma dai ba raddi mai zafi irin wannan gare ta ba.
Muryarta da ɗan zafi kaɗan take furta “Ai ke ce kullum sai ki yi ta goyon bayanta tana shuka mini rashin mutunci, komai na yi a gidan nan ba daidai ba ne, sam ba a ganin gwanintata ko ƙwazona aiki idan na yi yabon nata ne. Haba mama ki dinga adalci mana.”
Daga wannan furucin ba ta sake cewa komai ba sai ƙara cika da batsewa da take yi, a cikin zuciyarta tana ƙara jin tsanar Aishatu da kuma jin cewa ba za ta ƙara yin shiru ba a yanzu don kuwa sannu a hankali abubuwan da mama take yi mata na ɗora darajar ƙanwar a saman tata da ba ta dama ta ci mata zarafi a duk sanda ta so da ire-iren waɗannan ‘yan ƙananun abubuwan da ita maman ba ta ɗauke su a bakin komai ba su ne suka dinga taruwa sannu a hankali suka fara girma a cikin zuciyarta har suka yi ƙosawar da ta ji a yanzu ta ƙuna ba ta tarar ƙauri.
Maman ba ta iya cewa komai ba saboda guguwar mamakin sauyawar ɗabi’ar ‘yar tata na farat ɗaya, ba ta ji a ranta cewa kuskurenta ne ya haifar da hakan ba ta ɗauki laifin kacokan ta ɗaura shi a kan zafin rabuwa da Ahmad ne ya janyo sauyawar.
Ba jimawa Abbansu ya shigo gidan, ya yi tsaye kawai yana ƙare wa matarsa kallo ya lura cewa jikinta a sanyaye yake sai dai bai yi magana ba sai ita ce ta buɗe baki a sanyaye ta ce “Sannu da zuwa malam.”
“Yauwa, sannu da gida fatan kuna lafiya kamar yadda na bar ku.” Ya yi furucin idonsa a kanta, ta gyaɗa kai alamar eh.
Ya taka zuwa cikin ɗakin inda ya tarar da Surayyah ta rufe fuskarta da novel ɗin da ke riƙe a hannayenta biyu. Yana jiyo saukar numfashinta kaɗan-kaɗan wanda hakan ya ba shi tabbacin ba lafiya, cikin biyu dole a yi ɗaya ko dai kuka take ko kuma ba ta lafiya.
Taku uku ya yi ya isa inda take yana cire littafin daga kan fuskarta ya ga hawaye yana tsere a kan farantin kyakkyawar fuskarta mai kama da tashi sak. Duk cikin yaran nasa ba wanda ya kwashe kamanninsa kwabo da kwabo kamar ita sai dai shi yanzu don mayyanta da ya fara yi ma’aunin kyaunsa da hasken fatarsa ya yi ƙasa sosai a kan ita da take da jini a jika.
“Subhanallahi! Meke faruwa ne?”
Sai a lokacin ta buɗe idanunta da suke a rufe ta ɗago kanta ta daidaitu a zaunen da take ta saka hannu tana shafe hawayen da girgiza kai “Ba komai Abba, sannu da zuwa.” Ta ƙarashe tana sakar masa murmushin da zuciyarta ba ta aminta da shi ba.
Zaunawa ya yi a kan kujerar da ta ɗauke kanta ita kuwa ta ɗan matsa daga gefe don ta ba shi dama ya zauna da kyau.
“Ban yarda ba Surayyah! Ki faɗa mini gaskiya me ye matsalar? Wani ne yake takura miki a gidan nan?”
Ta girgiza kai alamar a’a kanta yana ƙasa.
Ya ja dogon numfashi ya sauke alamar akwai abin da ya taɓa masa zuciya kana ya fuskance ta cikin taushin murya ta rarrashi ya ce “Da ita, ki yi haƙuri da rayuwa Surayyah. Haka take cike da ƙalubale masu tarin yawa, a wannan duniyar farinciki kaɗan ne idan kika auna shi da yawan ƙunci da ɗacin zuciya da wahalhalu da suke zagaye da rayuwa. Jinkirin aure ba gazawarki ba ce ƙaddara ce ta kowa a rubuce take tun kafin zuwansa duniya. Ki toshe kunnuwanki daga duk kalamai marasa daɗi ki ci gaba da ibadarki da aka turo ki duniya don ita. Idan kika daka ta mutane za ki kai kanki ki baro ne kawai daga ƙarshe kuma su ne za su fara yi miki dariya.”
Ta gyaɗa kai tana furta “in sha Allahu Abba, na gode sosai.” Yauwa Allah ya yi miki albarka ya ƙara miki juriya. Ta shi ki kawo mini ruwa.”
Ta miƙe tana jin wata sabuwar ƙwarin gwuiwa tana shigarta. Kalamansa sun ƙara mata karsashin dagewa a kan addu’ar neman miji nagari da gujewa yin zaɓen tumun dare, saɓanin kalaman mahaifiyarta da a kowacce daƙiƙa suke aikin ruguza ƙarfin gwuiwarta da ingiza ta zuwa ga ɓarna.
Zuwa ta yi ta je ta ɗebo masa ruwan sha masu tsafta a kofin silver mai murfi ta kawo masa, a ciki ta tarar da mama a zaune tana buɗe masa kwanon abinci. Farar shinkafa ce da miyar tumatir ba ko nama a ciki, ta ɗauke kai daga kallon kwanon ta fita ranta cike da kyakkyawar fatar watarana ita ma za ta girkowa mahaifinta abinci da nama daga gidan mijinta.
Ubangiji mai sarrafa yanayi daga sanyi zuwa zafi, lafiya zuwa rashinta a lokacin ɗaya cikin yammacin wannan wunin ya jarrabi A’ishatu da rashin lafiya. Farat ɗaya zazzaɓi ya yi mata dirar mikiya ta rikice ta fita a hayyacinta sai mirgene-mirgene take har dare ya fara shiga mama ce kaɗai a kanta tana taimaka mata a duk lokacin da ta buƙaci hakan, ko kallon inda take kwance Surayyar ba ta yi ba ballantana ta yi mata sannu ko ta nuna tausayawarta a gare ta.
Zuciyarta na riƙe da wulaƙancin da suka yi mata a lokacin da kunama ta harbe ta abin ka da mai riƙo sam ba ta manta ba, a madadin ta yi afuwa sai ta ji cewar lallai sai ta rama ita ma A’ishatun ta ji inda daɗi.
Ita fa a zuciyarta yanzu ba ta jin ɗigon tausayin A’ishatu ba za ta ce ba ta ƙaunarta kwata-kwata ba don kuwa jininta ce amma dai ba ta jin wani motsin rai game da ita, a wurinta da wanzuwar A’ishan da akasinsa duk ɗaya, har ma ta fi yin farinciki idan ta wayi gari ba ta ji numfashin A’ishan a kusa da ita ba.
Tana gama sallar isha’i ta hau shirin tafiya maman ta kalle ta cike da ƙuluwa. “Wai ke ba ki ga halin da ‘yar’uwarki take ciki ba ne ba za ki yi mata sannu ba?”
Ɗauke kai gefe ta yi ƙasa-ƙasa ta furta “Allah ya ba ta lafiya.” Ta juya tana ci gaba da sabgogin gabanta maman ta sake cewa “Wai shirin zuwa ina kike yi tana cikin wannan yanayin?”
Ba ta juyo ba haka ba ta daina saka kayan da take yi a ƙaramar leda ba ta ce “Wurin kwanciya mana.”
“Gaskiya rashin tausayinki ya kai intiha Surayyah. Ke da ya kamata ki kwana a tare da ita ko za ta nemi wani abin cikin dare kin san dai ba wani ƙarfin kamata nake da shi ba.”
Daidai lokacin ta kammala shirinta ta miƙe tana furta. “Mama kin san dai gidan nan ya mana ƙarami sosai, tsakar gida ba za ta kwantu ba ga kuma Abba yana nan. Bar ta wannan ma gaskiya ba zan iya haɗa makwanci da ita ba ko da tana qalau kuwa. Sai da safe.”
Maman ba ta iya dakatar da ita ba sai raka ta da ido da ta yi har ta fice daga gidan. Tun jiya da suka samu matsala da Ahmad ta rasa gane kanta sam gabaki ɗaya ta gama sauyawa daga Surayyahn da ta sani a baya. Har tsawon wane lokaci za ta ɗauka kafin ta fita daga wannan yanayin? Tana fatan ba za a jima ba za ta warware domin ba za ta iya ci gaba da jure irin wannan rashin kunyar ba. A yanzu ma tausaya mata take saboda halin karyewar zuciya da take ciki.
BANGAREN HALISA
A ranar bai samu komawa gidansu yarinyar ba saboda yadda aikin assignment ɗin ya ci musu lokaci sosai su ne har 5pm suna shagon printing. Ko da aka gama aikin ya gama ƙaguwa da komawa hostel shi ya sa tun a ƙofar shagon ya yi sallama da Kasim ya tari mashin ya kai shi bus stop inda zai hau Bus ɗin makaranta. Tun daga wannan ranar kuma sai ya zamana ya yi busy sosai domin shirye-shiryen fara exam ɗin first semester da suke bai sake samun damar shigowa cikin gari ba sai a ranar hutun ƙarshen mako ya shirya tsaf cikin riga da wando na farin yadi mai taushi ya nufo cikin gari.
Ranar bai nemi Ƙasim ba kai tsaye gidan ya shiga lalube ya yi sa’a ya gane gun. A wannan kantin na ranar ya tsaya sai da ya jira layin ya ragu sannan ya kutsa kai ciki.
Da ya tabbatar an gama sallamar kowa ya miƙa masa hannu suka gaisa yana faɗar “sannu malam, na san ba ka shaida ni ba ko?”
Fuskarsa da fara’a ya gyaɗa kai alamar eh ya ce “Gaskiya ne.”
“Ni ne wanda na zo nan kwanan baya ina tambayarka game da yarinyar can gidan wacce ka ce ko Apsara sunanta?.”
“Oh! To na gane ka yanzu, me kake so?” Ya maida masa martani.
Ƙara nutsuwa ya yi muryarsa da taushi sosai ya furta “Ranar ka ce tana da kaka ba, idan ma na fahimta daidai a hannun kakar take. To don Allah sunan kakar za ka faɗa mini.”
Har a lokacin fara’ar fuskarsa ba ta gushe ba ya ce “Tabbas, sunan kakar Ige.”
“Yauwa na gode, yanzu zan tafi amma in sha Allahu duk sanda na shigo zan riƙa zuwa nan mu gaisa, ya sunan malamin?”
“Abdullahi, amma mutanen nan arear suna kirana da Maigwandu.”
Hannu ya miƙa masa suka yi musabahar bankwana yana faɗar “To, na gode malam Maigwandu, sai na sake zagayowa.”
Yana gama faɗa ya cire hannunsa a cikin na mutumin ya juya ya fita ya ƙarasa ƙofar gidan da ya ga ta shiga ranar ya tsaya yana tunanin abin yi.
Bai fi minti ɗaya da tsayuwa ba sai ga Affan ya fito daga cikin gidan hannunsa riƙe da ƙwallon tsumma da alama zai je gun wasa ne ya dakatar da shi da faɗar “Kai yaro zo nan.”
Ba tare da shayin komai ba Affan ya nufo wurin ya tsaya a gaban saurayin yana jiran jin me zai ce.
“Don Allah ka koma ciki ka ce ana sallama da Ige.”
Gyaɗa kai ya yi ba tare da yin magana ba ya juya da gudu ya shiga gidan yana ƙwala mata kira.
Daidai lokacin Ige tana sunkuye tana sharar tsakar gidan da dabara, don yi take tana zaunawa ta huta idan ta gaji. A hakan ma wai don ba daga sunkuye take yin sharar ba, ganin Affan ya shigo da gudu yana ƙwala mata kira ya sanya ta ajiye tsintsiyar hannunta ta kalle shi “Kai Affam lahiya dai kat shigo ma mutane da gudu haka?” Ta furta da hausarsu ta sakkwatanci da suke amfani da ita a jahar.
“Wani ne yana nan garka shi yac ce in kirawo mai ke.” Ya yi zancen yana gyara ball ɗin tsumman da ta fara warwarewa.
“Ka san shi ne?” Ta tambaye shi.
“A’a Ige ki dai je ki duba.” Iya abin da ya ce mata kenan ya fita da hanzari.
Kallon gefe ta yi alamun ta shiga nazari na ƴan sakanni kafin a hankali ta furta “Koma waye bari na je na ga da wacce ya zo.”
Ta wuce ɗaki ta janyo zanin atamfart’a da ke sarƙafe jikin rumfar gadonta ta yafa ta fita.
A cikin zauren ta same shi tsaye ya juya baya yana kallon waje ta matso kusa tana yi masa sallama.
Ya amsa a lokacin da yake juyowa. Kallon tsaf ta yi masa daga sama zuwa ƙasa sai dai ta kasa shaida shi da ma kuma ba ta cika riƙe fuskokin mutanen da suke nesa da ita ba saboda halin tsufa.
“Ɗan saurayi ban waye ka ba, ko za ka ba ni sani don Allah?”
Da fara’a a fuskarsa ya fara ƙoƙarin gaishe ta. “Kaka ina wuni, ya gida….?”
Nan da nan kuwa ta haɗe rai ta dakatar da shi da faɗar “Ka ga yaro bana son shaƙiyanci ka kira ni da Ige kawai idan kana neman zaman lafiya, amma wata kaka can ba daɗin ji.” Ta ɗauke kai gefe tana cuno baki.
Saura kaɗan dariya ta suɓuce masa don ya fahimci kamar tsohuwar ba ta son tsufa ne a cikin ransa ya ce ‘Ashe ga inda yarinyar nan ta yi gado, bar ta hali ma har kamanni a nan ta kwashe.’
A zahiri kuwa cewa ya yi “am to ki yi haƙuri. Tabbas ba ki sanni ba, sunana Muhsin na zo nan ne saboda jikarki.”
Ƙara tamke fuska ta yi don tana zargin ko ƙarar jikar tata ya kawo ta kuwa tabbatar ba za ta saurare shi ba domin jikarta tana sama da kowa a gun ta.
“To ina jin ka, Allah ya sa ba ƙararta ka kawo ba.”
“Sam ba ta yi mini laifin komai ba wata alfarma dai na zo roƙa wurinki a game da ita.”
“Oh to to! Yanzu na ji batu. Shigo mu je ciki ba na jure tsayuwa.”
Ba ta ba shi damar yin wata magana ba ta juya ta koma ciki, bisa ga tilas ya take sawayenta domin bai amayar da buƙatarsa ba kuma ba ya jin zai koma da ita tana tsikararsa a ciki.
Suna shiga ta shimfiɗa masa tabarma daga ƙarƙashin inuwa inda rana ba ta kai, ya zauna ita ma ta raɓe a gefe ɗaya tana cewa “To ina jin ka, wace alfarma ce?”
Jim ya yi na ɗan gajeren lokaci yana tunanin ya za ta kalli al’amarin daga mahangarta, da dai ya ga ta masa ƙuri ya buɗi ba ki ya ce “Da ma a kan wata jikarki ne an ce Apsara sunanta…”
Ba ta bar shi ya ƙarasa ba karɓe zancen “Kai bar jama’a shaƙiyancinta ne suke biye mata da shi amma sunan da ubanta ya raɗa mata shi ne Halisatu takwarata ce ai.” Ta ƙarasa furucin tana washe jajayen haƙoranta da suka rine da goro.
Murmushi ya ƙwace masa ya ce “To ita dai. Ina so ki ba ni dama na kasance jagoran rayuwarta, na kula da ita kamar yadda kowanne ɗan’uwa nagari zai kula da ‘yar’uwarsa.”
Ta buɗi baki kenan da nufin yin magana suka ji ƙarar faɗuwar bokitin ƙarfe a ƙasa kafin su yi wani motsi sautin ihunta ya ratsa masarrafar jinsu. Duka suka mayar da dubansu a ƙofar banɗakin da ke fuskantar su, inda take tsaye daga ita sai ɗaurin ƙirji ba ko ɗankwali a kai, jikinta jiƙe sharkaf da ruwa wanda hakan ke alamta daga wanka ta fito sai tsalle take tana zunduma ihu idanunta a rufe “Wayyo Allahna na mutu! Ige ki zo ki taimake ni.”
Ba ta daina tsallen ba hakan ba ta buɗe idanunta ba al’amarin da ya tilastawa Muhsin ɗauke idanunsa a kanta domin ya sani haramun ne a gare shi kallon tsiraicinta. Ga ta dirarriyar mace da halittunta suka fara cika a matsayin budurwa. Tsallen da take yi ya sanya duka gaɓoɓin jikinta suke motsawa ga shi kuwa Allah ya albarkace ta da wadatar dukiyar Fulani a ƙirji.
Ige ta yi wata iriyar zabura ta miƙe har tana shirin kifa ƙasa ta nufi inda take tana faɗar “Subhanallahi! Wai me ya faru ne kike mana ihu. Ke dai wallahi ban san sai yaushe za ki fuskanci kin girma ba haba.”
Da yatsa ta nuna mata ƙafarta ta dama inda bokitin ya daka da ƙarfi kafin ya faɗi ƙasa wanda ita da kanta sai a lokacin ta sunkuya tana duba wurin.
“Mtsw! Aikin kawai to ai wurin ko fashewa bai yi ba kin ishe ni da uban raki.” Ige ta yi furucin cike da haushi tana mai juyowa don dawowa inda ta tashi.
Sai a lokacin ta ɗago kanta idanunta suka sauka a kan fuskarsa lokacin da yake juyowa don jin motsi a kusa da shi.
Ta miƙe da ƙarfi tana fiddo ido waje ba tare da ta motsa daga gun ba ta ce “Wannan kamar tsololon nan na kwanan baya, na shiga ukuna!”
Ta yi furucin tana dafe ƙirji sannan ta kwasa da gudu ta shige ɗaki. Sosai ya yi dariya amma ba mai sauti ba ya mayar da hankalinsa kan tsohuwar don jin me za ta ce.
“To yaro aure kake nufi ko miye? Ban fahimce ka ba.”
Ya rusunar da kai ƙasa muryarsa da sanyi ya ce “Ba zan ce haka kai tsaye ba domin wannan ba iya hurumina ba ne ni kaɗai, amma ina mai tabbatar miki da manufar alkhairi na zo gare ku kuma in Sha Allahu ba zan taɓa cutar da ku ba. Ki ɗauke ni a matsayin jikanki, ki ba ni amanarta a matsayin ƙanwa tabbas zan kula miki da mutuncinta da tarbiyyarta.”
Har a lokacin ba ta san gurbin da za ta saka kalamansa ba amma ta ji ta amince da shi har cikin zuciyarta, duk da an ce mugu ba shi da kama ba ta ji a zuciyarta cewa wannan bawan Allahn zai siffantu da ɗabi’un mugaye ba don haka ta gyaɗa masa kai tana furta.
“Shi kenan, Allah ya ba ka damar riƙe alƙawarinka, bari na kira maka ƙanwar taka ku gaisa kafin in ƙarasa aikina in zo akwai tambayoyi da yawa da nake so na yi maka.”
Ta miƙe ta shige ɗakin can ba jimawa ta fito ta sunkuya ta ɗauki tsintsiyarta ta tsugunna tana mai ci gaba da sharar da ta soma.
Ko da ya lura da hakan ya miƙe cikin azama ya nufo inda take yana furta “Haba me kike yi hakan? Ina ƙanwata ne da ba za ta share miki ba.”
Ya ƙarasa furucin yana karɓe tsintsiyar hannunta. Ta miƙe tsaye tana faɗar “Tab! Wannan alanƙosa ɗin ce za ta yi shara? Ai ba ta ma iya ba idan ba shirme nake so na gani ba. Da dai shiririta ce da kallace-kallace to ita ce a sawun farko.”
Ya ji matuƙar mamakin hakan, ‘wai ba ta iya shara ba’ imagine a matsayinta na ya mace da take wannan matakin na girma. Lallai akwai babban aiki a gabansa matuƙar yana so ya sauke nauyin da ya ɗorawa kansa. Anyah kuwa zai iya? Kodayake da gwaji aka yi wa jirgi fiffike ya tashi don haka zai jarraba sa’arsa ya gani.
Wane nauyi ne Muhsin ya ɗorawa kansa a game da Halisa?
Shin Ige za ta yi nadamar buɗewa baƙo ƙofar gidanta da ba shi izinin zama ɗaya daga cikin ahalinta?
Al’amarin Surayyah fa ya gamayyarsu da mamanta za ta ƙare?
UMMU INTISAR CE



