Ɗan takarar gwamnan Jihar Sokoto na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Hon. Manir Dan’iya (Walin Sokoto), ya bayyana matuƙar damuwarsa kan rufe dukkan makarantun firamare da sakandare na gwamnati a ƙananan hukumomi 20 cikin 23 na Jihar Sokoto sakamakon matsalar rashin tsaro da ke ci gaba da addabar sassa da dama na jihar.
Ya bayyana wannan mataki a matsayin abin takaici da ke nuna irin munin matsalar rashin tsaro, duk da yawan tabbacin da Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Sokoto ke ci gaba da bayarwa cewa suna shawo kan matsalar. Ya lura cewa ƙananan hukumomin Sokoto Arewa, Sokoto Kudu da Wamakko ne kaɗai aka ware daga wannan umarni na rufe makarantu.
A cikin wata sanarwa da Mai Taimaka masa kan Harkokin Yaɗa Labarai, Aminu Abdullahi, ya fitar, Hon. Dan’iya ya ce rufe makarantun babbar koma baya ce ga ilimin dubban yara, domin hakan ya katse musu haƙƙinsu na samun ilimi kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanada.
Ya ce duk da cewa an ɗauki matakin ne domin kare rayukan ɗalibai da malamai, hakan ya nuna cewa rashin tsaro ya kai wani matsayi da gwamnati ba za ta iya ba da tabbacin tsaron yara a cikin makarantu ba. A cewarsa, babu wata al’umma da za ta samu ci gaba mai ɗorewa idan rashin tsaro ya tilasta rufe makarantu tare da hana yara samun ilimi.
Hon. Dan’iya ya tuna cewa matsalar rashin tsaro na daga cikin manyan batutuwan da suka bai wa jam’iyyar APC damar samun mulki a matakin tarayya da na Jihar Sokoto. Ya ce gwamnatin APC ta yi alƙawarin amfani da dukkan hanyoyin da suka dace domin dawo da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Sai dai, a cewarsa, duk da dimbin kuɗaɗen jama’a da gwamnatin tarayya da ta jihar suka samu cikin shekaru uku da suka gabata, matsalar rashin tsaro ta ci gaba da taɓarɓarewa, inda hare-hare, kashe-kashe, sace mutane, raba jama’a da muhallansu da kuma rufe makarantu suka zama ruwan dare a sassa da dama na jihar.
Dan takarar gwamnan na ADC ya bayyana cewa duk wata gwamnati da ta kasa kare rayuka da dukiyoyin al’umma ba ta cika ɗaya daga cikin manyan nauyin da Kundin Tsarin Mulki ya ɗora mata ba. Ya ce hana yara zuwa makaranta saboda rashin tsaro wata babbar shaida ce da ke nuna akwai buƙatar ɗaukar ƙwararan matakai cikin gaggawa, tare da inganta haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin dawo da zaman lafiya.
Ya tambayi irin abin da gwamnatin APC za ta gabatar wa al’ummar Sokoto a matsayin nasararta a yaƙin neman zaɓen shekarar 2027, alhali kuwa al’ummomi da dama na ci gaba da fuskantar rashin tsaro, katsewar karatu, matsin tattalin arziki da kuma rayuwa cikin tsoro.
Saboda haka, Hon. Dan’iya ya yi kira ga al’ummar Jihar Sokoto da daukacin ’yan Najeriya da su yi nazari kan halin da ƙasar ke ciki yayin da ake shirin babban zaɓen shekarar 2027. Ya ce dimokuraɗiyya ta bai wa jama’a damar tantance ayyukan waɗanda ke kan mulki tare da yanke hukunci ta hanyar akwatin zaɓe.
Ya buƙaci duk waɗanda suka cancanci yin zaɓe da su shiga harkokin dimokuraɗiyya cikin lumana tare da marawa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) baya, yana mai bayyana ta a matsayin sahihiyar madadin da ta himmatu wajen dawo da tsaro, farfaɗo da ilimi, inganta kiwon lafiya, samar da damammakin tattalin arziki da kuma tabbatar da shugabanci nagari, mai gaskiya da tausayi.
Hon. Dan’iya ya sake jaddada aniyarsa ta tabbatar da cewa kowane yaro a Jihar Sokoto ya samu damar yin karatu cikin yanayi mai cike da tsaro da kwanciyar hankali. Ya yi alƙawarin cewa idan al’ummar jihar suka ba shi dama a shekarar 2027, gwamnatinsa za ta ba da fifiko wajen dawo da zaman lafiya a faɗin jihar, kare makarantu, dawo da amincewar jama’a ga gwamnati da kuma aiwatar da ingantattun manufofi da za su tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi tare da samar da yanayin da zai bunƙasa ci gaba mai ɗorewa da walwalar al’umma.





