Rasa daya daga cikin shugabannin IZALA babban gibi ne aka samu a Nijeriya---Tambuwal

Rasa daya daga cikin shugabannin IZALA babban gibi ne aka samu a Nijeriya---Tambuwal

 

Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana rasuwar Farfesa Sani Aliyu Sagir mataimakin shugaban kungiyar Jama’atul Izalatil Bidi’a Wa’ikamatus Sunah na kasa, babban gibi ne aka samu a Nijeriya.

Tsohon Gwamnan Sakkwato Sanata Aminu Waziri Tambuwal a lokacin da yake ta’aziyar rasuwar margayin da ya rasu a jiya Assabar bayan rashin lafiya ta gajeren lokaci ya ce wannan rashi ne aka yi a Nijriya ba ga iyalai da 'yan uwa da kungiyar Izala ba kadai.

Sanata ya roki Allah ya gafartawa margayin ya kuma mika ta'aziyarsa ga iyalai da masoya da almajiran margayin.

Shaikh Yusuf Sambo Rigacukun amadadin shugaban majalisar malamai na kasa Shaikh Sani Yahaya Jingir ya karbi ta'aziyar ya kuma nemi Sanata Tambuwal da tallafawa gidan margayin ya samar da gurabun aiki ga diyan margayin domin su rike gidansu ba tare da wata takura ba.