Daga Muhammad Shamsudeen, Yobe.
Dan takarar Gwamnan jihar Yobe a karkashin jam'iyyar PDP a zaben 2023 mai zuwa, Hon. Shariff Abdullahi ya bayyana cewa ya na da ingantattun tsare-tsaren da gwamnatin sa za ta aiwatar matukar ya yi nasarar hawa karagar Gwamnan jihar, wadanda suka hada da aiki kafada da kafada matasa a jihar domin dora jihar bisa kyakkyawar turba; musamman ta hanyar zakulo hazikan matasan domin amfana da baiwar da Allah ya basu, inda jihar za ta ci gajiyarsu.
Hon. Shariff Abdullahi ya yi wannan furucin ne a sakon da ya aike wa matasan jihar Yobe a lokacin bikin Ranar Matasa Na Duniya a ranar 12 ga Agusta, 2022; wanda mai taimaka masa kan harkokin yada labaru, Mallam A. M. Mohammed, ya sanya wa hannu a ranar matasa ta duniya ta bana, ya ce muhimmin dalilin bikin na shekara-shekara wanda Majalisar Dinkin Duniya ke yi domin bai wa matasa muhimmancin da ya dace, inda ya yi alkawarin bai wa matasa cikakkiyar domin taka muhimmiyar rawa wajen samun ci gaba mai dorewa da gina Yobe sabuwa.
Ya ce a matsayin matasa daya daga cikin manyan kadarkon da kowace kasa za ta iya alfahari dashi, tare da kasancewar su shugabannin gobe, su ne a zahiri mafi girman jari kuma akalar ci gaban kowace al'umma. Matasa su ne ma'aunin gwargwadon kimar bunkasar duk wata kasa ko jihar da ta habaka a duniya, kana da yadda tasirin dorewarta zai kasance. Haka kuma ta hanyar kwazo, bajinta da sadaukarwarsu, tarbiyya da kyawawan halayensu, hadi da kishin kasa tare da hadin kansu ne kowace al'umma ke nema ruwa a jallo.
"Saboda haka za mu yi amfani da wannan dama wajen aiki da matasanmu domin su kasance tushen kayan aiki kuma jarin da za mu tanada wajen inganta jimillar dukan abubuwan da ake bukata don bunkasa jihar Yobe."
Matasa su ne ginshikin al’umma, domin karfinsu, kirkire-kirkire, dabi’unsu da sanin makamar tafiyar da al’umma. Ta hanyar fasahar kere-kere da karfin gwuiwa, jiharmu na samun gagarumin ci gaba a ci gaban tattalin arziki da ci gaban zamantakewa da siyasa. A cikin mafarkai da begensu, wata jiha ta sami kwarin gwiwarta; akan kuzarinsu, tana gina kuzarinta da manufarta.
"Har wala yau kuma, ba za mu yi wa matasanmu rikon sakainar kashi ba, face zamu yi duk abin da ya dace wajen gina matasanmu: su kasance masu gaskiya da rikon amana, aiki tukuru, masu tarbiyya da gina su bisa halaye nagari, su kasance masu kishin jiharmu, tausayi da sanin yakamata, riko da addini da al'adu nagari. Wanda ko shakka babu zai kasance sinadarin gina Yobe sabuwa kuma mai dorewa cikin mutunci da alfahari ga masu tasowa."
Sanarwar ta ci gaba da cewa, domin ya kamata matashi ya kasance mai gaskiya, ya nisanci cin hanci da rashawa, rashin da'a da duk wani aiki da ba zai so a jingina shi da shi ba. Ya ce a kokarin cusa gaskiya ga matasa, gwamnatin da zai kafa za ta rage yawan magudin jarrabawa a makarantu, wanda shi zai dakike rashawa a rayuwar matasa; domin duk yaron da zai yi magudi a jarrabawa tabbas ya na kan gabar rijiyar cin hanci da rashawa.
"Zamu cusa kishin jiharmu da Nijeriya baki daya a zukatan matasanmu, saboda matashi mai kishin kasa ba zai tsunduma cikin almundahana ba domin ya san cin hanci da rashawa na da illa ga ci gaban kasa. Don haka matashi ya kamata ya yi abubuwan da za su inganta sunan danginsa, al'ummarsa, kananan hukumomi, jiharsa da kuma kasarsa."
A karshe, dan takarar Gwamnan jihar ya bukaci matasan jihar su guji tsunduma cikin aikata laifukan da dokokin kasa suka yi hani irin su bangar siyasa da shan abubuwa masu sanya maye. Ya ce su rinka yin kaffa-kaffa da wasu yan siyasa masu ingiza matasa shiga ayyukan tarzoma ko tada zaune tsaye don biyan bukatun kansu, "Maimakon hakan, ina kara kira ga matasanmu a jihar Yobe su rungumi sana'a da noma da kiyo, kuma kar kuyi wasa wajen neman ilimin boko da na addini, ku kyautata wa mahaifa da ci gaba da bai wa gwamnatin goyon baya."