Ranar Masu Lalura Ta Musamman: Kungiyar Jam'iyar Matan Arewa Ta Raba Kayan Karatu a Zamfara

Jam'iyar Matan Arewa ta kasance kungiyar da bata gwamnati ba wadda ke taimakon Marayu da marasa karfi dake fadin jihar nan

Ranar Masu Lalura Ta Musamman: Kungiyar Jam'iyar Matan Arewa Ta Raba Kayan Karatu a Zamfara

Kungiyar  Jam'iyar Matan Arewa reshen jihar Zamfara ta raba kayan karatu ga dalibban makarantar koyar da masu lalura ta musamman dake Gusau cikin murnar zagayowar ranar masu lalura  ta duniya ta wannan shekarar 2023.

Da take jawabi a lokacin taron raba kayan shugabar kungiyar Hajiya Maryam Rufa'i Nadama tace manufar wannan karamcin shi ne domin karfafama lamurran su.

Ta ce Jam'iyar Matan Arewa ta kasance kungiyar da bata gwamnati ba wadda ke taimakon Marayu da marasa karfi dake fadin jihar nan.

Hajiya Maryam Rufa'i Nadama tayi kira ga wadan da suka amfana da suyi amfani da kayan ta hanyar data dace.

A wata mai kama da wannan kungiyar ta raba barguna, sabulu da kuma gidan sauro ga 'yan gudun hijira dake Saminaka a Gusau Babban birnin jihar Zamfara.

Da take jawabi a wajan taron rabon kayan Shugabar Kungiyar Hajiya Maryam Rufa'i ta jajanta masu bisa hare haren yan bindiga a yankunan su.