Ran matasan Nijeriya a ɓace ya ke kan 'baƙin mulki' da ake a ƙasar - Obasanjo 

Ran matasan Nijeriya a ɓace ya ke kan 'baƙin mulki' da ake a ƙasar - Obasanjo 
 
Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya yi gargadin cewa akwai karuwar rashin jin daɗi a tsakanin matasan Najeriya sakamakon mulkin da ya dade yana tafiya ba daidai ba.
 
Jaridar The Punch ta rawaito cewa Obasanjo ya ce sai dai idan shugabanni sun canza salon mulkinsu, amma idan ba haka ba to babu makawa za a fuskanci juyin juya hali da matasan da ke fama da yunwa da kuma fushi za su jagoranta.
 
A cewarsa, ko da yake Najeriya tana da matasa masu hazaka da aiki tukuru, amma yawancin su sun yanke kauna da yadda ake tafiyar da dukiyar ƙasa, rashawa mai yawa, da kuma gazawar shugabanni wajen mulki.
 
Obasanjo ya bayyana wannan a cikin ɗaya daga cikin sababbin littattafansa mai taken ‘Nigeria: Past and Future’ wanda aka kaddamar a makon da ya gabata.
 
Tsohon Shugaban Kasar ya ce shugabanni a nahiyar Afirka kada su yi tunanin za su ci gaba da mulki da sata a fili da kuma yaudarar jama’a, suna nuna halin ko in kula ga wahalhalun talakawa ba tare da fuskantar tasgaro ko tarzoma ba.
 
Ya ce, “Yanayin da ake ciki a nahiyar na nuna cewa matasa sun fi kowane lokaci sanin hakkinsu, ba sa hakuri da cin zarafi ko amfani da karfin mulki ba daidai ba, kuma suna bukatar amfanin nagartaccen shugabanci. Don haka, ko mun yarda ko ba mu yarda ba, akwai wata gagarumar girgiza da ke tafe.”