Ramadan:Gwamnan Kebbi Ya Shirya Ciyar Da Talakawa Abinci

Ramadan:Gwamnan Kebbi Ya Shirya Ciyar Da Talakawa Abinci

Gwamnan jihar kebbi Kwamred Nasir Idris ya shirya rabon abinci kyauta a watan azumin Ramadan mai zuwa.

Kwamred Nasir Idris Kauran Gwandu  ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta dauki akalla masallaci daya a kowace karamar hukuma domin ciyar da jama'a abinci kyauta a watan Ramadan gwamnan ya fadi wannan shiri ne yayin da ya karbi bakuncin tawagar wakilan kananan hukumomi biyu a ranar Litinin.

Masu sharhi na ganin shirin Wani abu ne Mai kyau, sai da yawan abincin yayi kadan ganin halin da ake ciki na tsadar rayuwa.

Masana sun shawarci gwamnati da ta duba yiwuwar Kara yawan wurin ciyarwar don hakan kawai zai sa kwalliya ta biya kudin sabulu.

 Abbakar Aleeyu Anache