Ramadan: Malamin Addini Yayi Kira Ga CBN a Saki Takardun Kuɗi Isassu 

Ramadan: Malamin Addini Yayi Kira Ga CBN a Saki Takardun Kuɗi Isassu 

 

Yayin da watan Ramadana mai albarka ke ƙara ƙaratowa, mutane na cigaba da kiraye kiraye ga babban bankin Najeriya daya ci gaba da sakin kuɗi isassu domin walwala. 

Ɗaya daga cikin mutanen dake kiranye kiranyen sun haɗa da shahararren malamin addinin Muslunci nan mai suna Nurul Yaqeen na masallacin Jumma’a dake Life Camp, Abuja. 
Malamin yayi kira ga bankin ne da ya saki isassun kuɗaɗe sababbi duba da yadda watan Ramadan mai albarka yake tunkarowa. 
Al-Yolawi yayi kiran ne a yayin da yake huɗubar juma'a akan maudu'in "Amfanin Azumin Watan Ramadan: Ga Lafiya, Mu'amala, Hankali da Ruhi " ranar juma'a a Abuja. 
Malamin ya ce, musulmi suna kashe kuɗi sosai a watan Ramadan wajen sayen abinci da kayan da zasuyi sadaka dasu, wanda yake faruwa sakamakon tsari, shiri na kasafin kudin aljihu akan yadda za'a kashe su.  
"Hakan ya ta'allaƙa da yadda kuɗi yake shiga da fita daga hannun mutane ɗaiɗaiku da ƙungiyoyi, kuma hakan nada muhimmanci sosai ga harkar saye da sayarwa. Ci gaba da wanann salo, bayan ramadan yana da tasiri sosai wajen haɓaka kasuwancin ku".