A ƙoƙarin gwamnatin jihar Sakkwato na ganin ma’aikata sun fara ibadar Azumin Ramadan cikin sauƙi, Gwamna Ahmed Aliyu ya amince da gaggawa a fara biyan albashin watan Fabrairu a 2026 daga ranar juma’a 13 ga watan.
Biyan albashin kamar yadda aka saba ya shafi ma’aikatan jiha da ƙananan hukumomi da malaman Firamare da masu karɓar Fansho a faɗin jiha.
Gwamna Ahmad ya yi kira ga ma’aikata su dubi wannan hoɓɓasar ta gwamnati su tsaya su yi aiki cikin gaskiya da amana.
A bayanin da babban direkta na yaɗa labarai a ofishin Gwamna Alhaji Abubakar Bawa ya fitar a Alhamis ya ce Gwamna ya ƙara bayar da tabbacin gwamnatin sa na tsaye kai da fata a tabbatar da ruhin aikin gwamnati ya cigaba da wanzuwa a jiha haka ma ya godewa mutanen jiha kan goyon baya da addu’oin da suke wa gwamnatinsa.
Malam Murtala Bello Ɗa’a ma’aikaci ne jiha ya ce Gwamnati Sakkwato ta kyauta ta yi abin alheri sai dai akwai abin da yakamata a yiwa ma’aikata fiye da wannan.
“Ma’aikatan ya fi dacewa a ba su rabin albashi kyauta domin alfarmar watan Ramadan, ganin duk wasu kuɗaɗe da jiha ke samu ma’aikatan gwamnati ne ginshiƙin samun, kyautata masu abu ne da yakamata.
“In har za a baiwa ‘yan siyasa kayan azumi da suka shafi shinkafa da Suga da Madara, wasu har da gero a kyauta, in babbar Sallah ta zo a basu raguna, shi ma ma’aikaci a shekara yakama ya samu kyautar ko rabin albashinsa ne daga gwamnati,” kalaman Malam Murtala Ɗa’a.
Kasimu Shehu ya ce wannan biyan albashi an yi shi ne don a rikita su ga yanda suka saba tafiyar da rayuwarsu a tsare, kowa yasan albashi baya wadatar da ma’aikaci a yanzu kan haka ya dace gwamnati ta fito da shiraruwan tallafawa ma’aikata a lokutan ibadar Azumi da Sallah.
Ya ce ma’aikaci na buƙatar tallafin gwamnati kamar yadda suke taimakawa wasu jama’a, “a yanzu da Azumin Ramadan ya shigo Gwamnatin jihar Sakkwato sai ta kashe kuɗi fiye da rabin yawan kuɗin da ake biyan albashi da su wajen rabawa mutane abinci a kyauta ka ga ya dace a ma’aikata su shiga cikin tsarin su amfana amma ba a yi, sai dai a zura masu ido tun da ana biyansu albashi.
“Za ka samu wasu jihohi a Kudu suna ba da kyautar albashi a lokacin Kirsimeti ko anan ya dace gwamnoninmu su kawo wannan tsarin zai taimaki aikin da bunƙasar tattalin arzikin jiha,” in ji shi.






