Raɗe-raɗen Rashin Lafiyar Tinubu Mataimakin Sakataren Yada Labarai Ya Yi Magana Kan Batun
Raɗe-raɗen Rashin Lafiyar Tinubu Mataimakin Sakataren Yada Labarai Ya Yi Magana
Mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar APC, Yakubu Murtala Ajaka, ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Sanata Bola Ahmed Tinubu yana cikin koshin lafiya ba wai ya tafi jinya kamar yadda a ke yada wa.
Ajaka, wanda ya ziyarci Tinubun a birnin Landan, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yammacin jiya Lahadi.
Ya ce, “Saɓanin jita-jitar da ake ta yaɗa wa a fili wanda ƴan adawar siyasarmu su ka rika yaɗa wa cewa Sanata Bola Ahmed Tinubu ya tafi jinya a Landan. Karya ce gaba daya”.
Ya bayyana cewa Sanata Tinubu ya je kasar ne domin ganawa da kungiyoyi daban-daban domin ci gaban kasar, yana mai cewa shi ‘mai ɗa’a ne ga ƙasa.
Ya kara da cewa Tinubu mutum ne mai cike da gogewa a harkokin siyasa da gudanarwa, wanda ke da cikakkiyar fahimta game da bambance-bambancen Najeriya kuma zai tura wannan ilimin zuwa jagoranci idan aka zabe shi.
Ya jaddada cewa a cikin wasu abubuwa, dan takarar shugaban kasa zai yi amfani da damarsa wajen haɗa kan al’umma da hada kan matasa domin tafiyar da manufofin kasar nan.
Hon. Ajaka ya kara da cewa, a cikin waɗanda za su fafata a zaben shugaban kasar tarayyar Najeriya a zaben 2023, dan takarar jam'iyyar APC ya fi kowa damar lashe zaɓen.
managarciya