PDP za ta ƙaddamar da Kwamitin karɓa-karɓa a wani sati

PDP za ta ƙaddamar da Kwamitin karɓa-karɓa a wani sati

Domin samar da mafita da kashe wutar rigimar da ta taso a jam'iyar PDP saboda takarar shugaban ƙasa shugabannin jam'iyar PDP za su ƙaddamar da kwamitin karɓa-karɓa wanda zai raba muƙaman shugabancin jam'iya a yankunan Nijeriya.

An samu bayanin ne a tattaunawar manema labarai da mataimakin shugaban jam'iyar Alhaji Shu'aibu Oyedokun ya fitar da cewa kafa kwamitin ya biyo bayan matsayar da aka cimma a taron gaggawa da PDP ta yi.

A cewarsa matsayar kafa keamitin ta zo ne kan rikita-rikitar da ke akwai a tsakanin 'yan Nijeriya.

Ya ce dayawan 'yan Nijeriya ba 'yan siyasa kawai ba suna maganar sun matsu su ga wane yanki  ne manyan jam'iyyun siyasa guda biyu APC da PDP za su kai takarar shugabancin ƙasa a 2023 kudu ko Arewa. Hakan ya sanya jam'iyar PDP take son warware matsalar kafin babban taron ƙasa da za a yi watan Okotoba.

Ya ce Wani sati za a ƙaddamar da kwamitin PDP za ta yi adalci da gaskiya da fatan mambobin kwamitin da za a ƙaddamar  su yi adalci ga aikin da aka ba su.