Home Siyasa PDP ta amince da Pantami da wasu mutum biyu su fafata a...

PDP ta amince da Pantami da wasu mutum biyu su fafata a zaɓen fidda gwani a Gombe

2
0

Jam’iyyar PDP a Jihar Gombe ta amince da Farfesa Isa Ali Pantami, Khamisu Ahmed Mailantarki da Usman Aliyu Garry su fafata a sabon zaben fidda gwani na takarar gwamnan jihar.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar a jihar, Abdulkadir Ahmed Dukku, ya fitar ranar Juma’a, ya ce an amince da ’yan takarar uku domin shiga sabon zaben fidda gwani.

Jam’iyyar ta ce za a gudanar da sabon zaben ne a Talata, 29 ga Satumba, 2026, inda ta buƙaci dukkan mambobin da suka cancanta su taru a yankunansu na mazabu domin zaɓar ɗan takarar da suke so.

Wannan mataki ya biyo bayan hukuncin kotu da ya soke nasarar Pantami a zaben fidda gwanin da aka gudanar a baya, tare da umartar PDP da ta gudanar da sabon zabe.

PDP ta ce ta karɓi hukuncin kotun cikin kyakkyawar fahimta, kuma za ta mutunta shi.

Sabon zaben na nufin Pantami, wanda a baya ya samu tikitin PDP, zai sake fafatawa da Mailantarki da Garry domin neman tikitin jam’iyyar na zaɓen gwamnan Gombe na 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here