Shuwagabannin kungiyar kwadago ta kasa NLC, sun bayyana wasu sharudda shida da ya zama wajibi a cika su kafin kungiyoyin kwadago a kasar su janye yajin aikin da suke yi.
Sun jera sharuddan shida a cikin wata sanarwa da suka fitar a shafin kungiyar na X (wanda aka fi sani da Twitter) ranar Talata.
Kungiyar ta NLC ta ce, da farko dole ne a kama Chinasa Nwaneri, mai ba Gwamnan Imo shawara, da ake zargin shi ne ya jagoranci harin da aka kaiwa shugaban NLC da sauran ma’aikata a jihar, tare da kai shi gaban kotu.
Kungiyar ta kuma ce a kama dukkan jami’an ‘yan sanda da kuma ‘yan daba da ke da hannu a harin da aka kai wa shugaban kungiyar, a gurfanar da su gaban kuliya tare da korarsu daga aiki. Haka kuma, ta bukaci a kama, gurfanarwa tare da korar babban jami’in tsaro a gidan gwamnatin jihar Imo, wanda aka fi sani da SP Shaba. “Ya jagoranta tare da bayar da mafaka ga ‘yan daba don muzgunawa ma’aikata a jihar Imo,” NLC ta yi zargin.
Wani sharadi da kungiyar kwadago ta bayar shi ne kamawa, hukuntawa da kuma korar wani kwamandan ‘yan sandan da ba a bayyana sunansa ba, wanda ta ce shi ne ya ba da damar cin zarafin shugaban NLC da sauran ma’aikata a jihar. Sharadi na shida don kawo zaman lafiya shi ne cewa, dole ne a binciki tsohon kwamishinan ‘yan sandan jihar Imo, Ahmed Barde, tare da gurfanar da shi a gaban kuliya bisa zarginsa da hannu wajen cin zarafin shugaban NLC. “Bukatunmu masu sauki ne. Muna neman adalci". - Cewar NLC
Kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito, kungiyoyin kwadago na Najeriya NLC da TUC, sun umurci mambobinsu da su fara yajin aiki a fadin kasar, sakamakon harin da aka kaiwa shugaban NLC, Joe Ajaero.