Nijeriya@61: Son Zuciya Da Rashin Iya Mulki Yasa A Kullun Kasar Ke Baya- Nasko

Wajibi Shugaban Kasa Ya Kawar Da Banbancin Siyasar Da Ke Tsakaninsa Da Manyan Kasar Dan Samun Nasara A Sauran Wa'adin Da Ya Rage Mai.

Nijeriya@61: Son Zuciya Da Rashin Iya Mulki Yasa A Kullun Kasar Ke Baya- Nasko
Nijeriya@61: Son Zuciya Da Rashin Iya Mulki Yasa A Kullun Kasar Ke Baya- Nasko
Shekaru 61 Da Samun Yancin Kai;
Wahalhalun Shekaru Biyu Da Al'umma Suka Fuskanta Yasa Sun Manta Da Nasarorin Da Aka Samu- Wanna
* Son Zuciya Da Rashin Iya Mulki Yasa A Kullun Kasar Ke Baya- Nasko
* Wajibi Shugaban Kasa Ya Kawar Da Banbancin Siyasar Da Ke Tsakaninsa Da Manyan Kasar Dan Samun Nasara A Sauran Wa'adin Da Ya Rage Mai
Daga Babangida Bisallah, Minna
Ranar juma'ar nan da yayi daidai da daya ga watan Oktoban 2021, Najeriya ke cika shekaru sittin da samun yancin kai, tun da farko bayan kammala jawabin shugaban kasa ga yan Najeriya kan bukin wannan ranar, masana da dama sun tofa albarkacin bakin su kan jawabin na shugaban kasa.
Alhaji Awaisu Muhammad Wanna, gogaggen dan siyasar da suka yi gwagwarmayar ganin an kori soja daga madafun ikon kasar nan ta hanyar dawo wa kan tafarkin mulkin dimukuradiyya. Yace maganar cigaba ko samun nasarar a cikin shekaru sittin da samun yancin kai abin dariya ne musamman a wannan zangon na shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin idan ana maganar cigaba ana magana ne akan zaman lafiya, hadin kai da fahimtar juna tsakanin yan kasa.
Amma abin bakin ciki idan ka dubi irin turbar da tsoffin shugabannin da suka yi gwagwarmayar ganin kasar ta samu yancin, an kaucewa ma wannan turbar, yau a kasar nan an koma maganar yanki ba kasa ba, bayan nan rashin tsaro maimakon yayi baya sai gaba yake yi.
Musamman shekaru biyu din nan daga bara zuwa bana hasarar da kasar nan ta tafka ya wuce tunani, tattalin arzikin kasar a kullu yaumin sai baya yake, sannan rayukan yan kasa ba a bakin komai yake domin baka tabbas akan za ka iya rayuwa idan ka wayi gari kuma kullun gwamnatin sai hankoron cewar take tana daukar matakai.
Tunda farko an baro gini ne tun ranar zane, kasar Ingila ce ta yantar da mu, amma mun ce muna tsarin tafiyar da mulki ne irin na kasar amurka, muna da kundin dokokin tafiyar da mulki, amma dukkan su ba a tafiyar da shugabanci akan wannan tsarin, ka ga ke nan ba lallai ba ne mu ga daidaito ba a shugabancin kasar nan ba.
Idan mun dubi tsarin tafiyar da tsaron mu tun farko akwai gyara, soja da aka san shi a fagen yaki an bar shi yasan dadin mulki, kan haka ne yasa tsoffin sojoji suka mamaye bangaren shawarwari kan lamurran tsaro, wanda idan ka dubi sauran kasashen duniya akan zakulo gogaggun masana ne da suka san lamurran tsaro suna bada shawarwari kuma ake samun nasara. Ya kamata wa'adin da ya rage wa shugaba Muhammadu Buhari yayi anfani da shi wajen kyautata lamurran tsaro.
Kasar da ke da adadin mutane sama da miliyan dari uku a ce wai duk shekara za a dauki jami'an yan sanda dubu goma da ake kyautata zaton kafin 2022  za a samar da jami'an yan sanda dubu ashirin, idan ka dubi gurbin da ake bukatar cikewa yanzu yafi wannan adadin da ake tunanin dauka.
Alhaji Musa Aliyu Liman, shi ne shugaban jam'iyyar APGA a jihar Neja. Yace lallai wannan rana ta yau rana ce ta bakin ciki da zubar da hawaye, domin mai makon kasar nan ta cigaba a bangarori da dama sai ta samu kan ta a cikin wani mayucin hali na rashin tabbas ga rayuwa.
Idan mun yi la'akari da halin rashin tsaro, rashin kayan more rayuwa, musamman bangaren kiwon lafiya da hanyoyi da a kullun ke janyo hasara ga al'ummar kasar abin takaici ne. Misali yau mutumin karkara da ya saba rayuwarsa wajen noma da kiwo tilasta ta sa ya bar inda yake zauna ya zama dan gudun hijira, wannan koma baya ne sosai ba cigaban da za a yi murna ba.
Idan ka dawo bangaren hanyoyi, ka dauki jihar Neja da take kusan itace jihar da ta zamo mahada ga sauran jahohin arewacin kasar nan da ke sada mu da kudanci, kuma tafi kowace jiha hanyoyi mallakin gwamnatin tarayya amma an wayi gari saboda son zuciya da bambancin siyasar da ke tsakanin tsoffin shugabannin da suka gaba da masu mulki yanzu ya jefa matafiya cikin hadari na hasarar dukiyoyin su saboda kin sauke nauyin gwamnatin tarayya akan al'ummar kasa.
Tun zuwan gwamnatin nan tayi alkawalin gyaran hanyoyin amma tayi watsi da su da ya kai ga direbobin manyan motoci yin rufe hanyoyin saboda yawaitan hadura da hasarar da suke yi duk da irin kudaden shigar da gwamnatin tarayya ke anfana daga gare su.
Wajibin shugaban kasa ne, ya tuna cewar talakawa sun zabe shi ne saboda kyakkyawar zaton alherin da suka yi akan shi, wanda yau saboda wata matsala ta daban yasa ya manta irin alherin da talakawan kasa musamman ma na jihar nan suka yi mai na ba shi damar shugabantar kasar nan.
Lokaci yayi da shugaba Muhammadu Buhari zai kauda wannan tunanin ya ceto al'ummar kasar nan daga wannan yanayin na fargaba da ceto rayukan su daga salwanta akan hanyoyin nan, domin ni a tunani na ba wani jawabin da ya kamata ya tsaya yana yi illa mu ga aiki a kasa.
Kwamred Musa Adamu Nasko, shi ne shugaban kungiyar masu hakar ma'adinan kasa a jihar Neja. Yace Najeriya ta rasa alkibla, domin maimakon bashin da ta ke jajibowa kasar nan, da ta fadada zuwa wasu bangarorin ma'adinan kasa, ba sai ta jira abinda ke shigowa daga man fetur ba.
Gwamnatin tarayya ce ke da alhakin kula da ma'adanan kasa, amma saboda rashin kwarewa da rashin sanin muhimmancin arzikin da Allah ya baiwa kasar nan da gyaran ake son yi da gaske ba sai mun ciwo ba shi ba, domin duk wani abinda wata kasa take alfahari da shi kuma ta dogara akan shi Najeriya muna da lunkin shi kuma wanda yafi na ta tasiri.
Ana maganar hare haren da ake kaiwa al'ummar karkara da cewar masu wannan mugun dabi'ar masu hakar ma'adinai ne, wannan kuskuren fahimta ne, domin dan ma'adinan kasa bai san komai ba face rika shebur da gwamgiri wajen yin ninkaya cikin arzikin da Allah ya shinfida a kasa dan neman abinci.
Kawai sakaci da mummunar siyasar da aka sanya a gaba, yasa aka bar ganga ana bugun taiki. Saboda haka matsalar rashin tsaro gwamnati ta san inda abin yake, kuma ta sani itace ke da alhakin magance shi. Yau saboda wannan matsalar tsarin ilimi ya tabarbare, an rarraba kawunan yan kasa, yarda da soyayyar juna ya kau to yaushe za mu tsaya yaudarar kan mu da sunan murnar samun yancin kai.
Yau idan ka fito ka ce ga kuskure sai a ce kai dan adawa ne, sai a ce wai kana yiwa kasa zagon kasa, wannan kasawa ce da ya kamata a yi azaman farkawa daga dogon baccin da ake yi.
Idan kasar nan ta tarwatse ba mu da wurin zuwa, idan muka ka sa samun shugabanni masu kishin kasa to mu sani halin da muka samu kan mu a yanzu sai ya wuce haka.
Ina baiwa gwamnatin tarayya da na jahohi shawara da su ji tsoron Allah su farka daga baccin da suke yi wanda yasa rashawa mai makon tayi baya a kullun gaba ta ke, su kirkiro hanyoyin dogaro da kai ta hanyar samarwa jama'a ayyukan yi ba sai mun dogara da aikin gwamnati ba 
Kamar yadda na bayyana a baya muna da din bin ma'adanan kasa masu albarka da za a mayar da hankali akan su wajen samun kudaden ayyuka ga kasa da karfafa guiwar yan kasa wajen dogaro da kai. Mu nemo masu hali su zuba jari wajen hakar ma'adanan shi zai baiwa kasar damar samun karfin guiwar tsayawa da kafarta wajen samar Najeriya nagartacciya.