NEMA ta fitar da gawar mutum 3 a Sokoto

Hukumar bayar da agajin gaggawa reshen jihar Sakkwato(MEMA) ta fitar da gawar mutum uku a cikin 25 da suka bata bayan jirgin ruwa ya nutse a karamar hukumar Goronyo a satin da ya gabata.
Hukumar ta ce bayan gano gawar guda uku a ranar Talata bincike zai cigaba har ga ko za a iya samun wasu mutanen bayan wadan nan da suka nutse a gulbin Kojiyo da Bari da  Wuci a karkashin hadin guiwa NEMA da hukumar kula da gulabe NIWA da ta agajin gaggawa ta jiha SEMA da Masunta masu shiga ruwa a yanzu mutanen da ba a gani ba su 22 ne.
Aliyu Shehu Kafindangi ne ya jagoranci tawagar tare da goyon bayan sojojin sama a bangaren su na kula masibbu, ana daukar matakan da suka kamata na rage yawan ruwan da sauran dubaru.
NEMA ta ba da tabbacin cigaba da binciken har kwalliya ta biya kudin sabulu.
An yi wa gawar uku sallah a binne su kamar yadda Shari'a ta tanadar.