Natasha ta sanar da ranar da za ta dawo zaman majalisar dattawa
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, shugabar kwamitin majalisar dattawa kan harkokin ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje da ƙungiyoyin masu zaman kansu (NGOs), ta bayyana cewa za ta koma bakin aikinta na majalisa a gobe Talata, bayan hukuncin kotu da ya soke dakatar da ita.
Yayin da ta ke jawabi ga magoya bayanta cikin wata bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, Natasha , wacce ke wakiltar Kogi ta tsakiya ta nuna godiya ga goyon bayan da suka ba ta.
Ta ce: “Na gode da goyon bayan da kuka bani. Ina murna da nasarar da muka samu yau. Da yardar Allah zan koma majalisa a ranar Talata.”
A ranar Juma’a da ta gabata ne dai wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke hukunci cewa dakatar da Natasha na tsawon watanni shida da majalisar ta yi ya yi yawa kuma ba bisa doka ba ne kuma ya tauye ’yancin wakilcin mazabarta.
Daga nan ne kotu ta umarci a mayar da ita nan take.
Sai dai kotun ta ci tarar Sanata Akpoti-Uduaghan Naira miliyan biyar (₦5m) saboda laifin raini ga kotu, sakamakon wani rubutu da ta wallafa a Facebook wanda ya sabawa umarnin kotu na baya.
Mai shari’a Binta Nyako ta bayyana cewa rubutun nata — wanda ya kasance kamar habaici ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio — ya saba wa umarnin kotun na 4 ga Maris, 2025 wanda ya hana kowane bangare yin magana a bainar jama’a ko a shafukan sada zumunta game da shari’ar.
managarciya