Mutanen Sakkwato ta Gabas sun roki Gwamnati ta shiga tsakaninsu da Bello Turji

Mutanen Sakkwato ta Gabas sun roki Gwamnati ta shiga tsakaninsu da Bello Turji

Mutanen karamar hukumar Isa a jihar Sakkwato sun nuna damuwarsu kan wa'adin da dan bindiga Bello Turji ya ba su kan dole sai sun bar garuruwansu na asali su yi kaura don baya bukatar ganinsu a wuraren, ya tayar da su.

Dan bindiga Bello Turji a farkon satin nan aka samu labarin ya bayar da umarni ga mutanen karamar hukumar sai sun gina wani karamin gulbi(dam) ko su fuskanci hukunci.

Wasu mazauna karamar hukuma ta Isa sun yi magana da manema labarai a satin nan in da suke rokon gwamnatin jiha da jami'an tsaro su kare su ga harin Turji ganin yanda garin Isa yake da yawan jama'a da kasar noma.

Wanzami Abubakar Isa ya bayyana wa'adin da aka ba su abin damuwa ne akwai bukatar gaggauta daukar mataki.

Ya ce "abin mamaki ne yanda ake yi mana a kasar mu ta haihuwa kamar wasu baki, duba yanda 'yan bindiga ke ba mu umarni da wa'adi a garuruwanmu  yanda  za mu yi rayuwarmu,"  ya nuna maimakonsa.

"Muna kira ga gwamnati ta tseratar da mu ga halin da muka tsinci kanmu a ciki, lamarin 'yan bindiga yakai muna matuka ya sa rayuwar mu ta tabarbare kamar mu ba mutane ba ne a in da muke zaune muna bukatar kwanciyar hankali a yankinmu."

Alhjaji Abdullahi Isa ya ce yanayin ya kai makurar da sai an nemi gwamnati ta dauki matakin da ya kamata, "muna shan bakar wuya a kasar mu, abin da ba za mu lamunta ba don ba mu san in da za mu tafi ba, ta yaya za mu bar gidajenmu mu gudu saboda Bello Turji don haka gwamnati ta yi wani abu."

Bashar Ahmad ya roki gwamnatin Sakkwato da tarayya su yi wani abu kan wa'adin nan bai kamata su kyale Turji na cin karensa ba babbaka ba.

"Gwamnati ta kyale mu da 'yan bindiga suna yi mana yanda suke so wanda hakan abin an karar da su ne su yi wani abu don kwatar mana da 'yancinmu".

Duk yunkurin jin ta bakin shugaban karamar hukumar Isa Alhaji Sharifu Kamarawa da mai baiwa gwamna shawara kan harkar tsaro Ahmad Usman, bai yi nasara ba dukansu kira da aika sakon da aka yi masu ba su mayar da amsa ba har zuwa hada rahoton.

A bayanin da aka samu Turji bai ayyana wata rana da zai kawo hari in mutanen ba su tashi ba amma dai akwai fargaba da ganin ya kamata gwamnati ta yi wani abu sabanin sulhun da take raya za ta yi da 'yan bindigar yankin Sakkwato ta gabas.