Home Labarai Sarkin Musulmi baya da ɗan takara a zaɓen 2027

Sarkin Musulmi baya da ɗan takara a zaɓen 2027

20
0

Hankalin masu kula da harkokin yaɗa labarai na Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya karkato kan wani rahoto da ke yawo a kafofin sada zumunta cewa Sarkin Musulmi ya yi kira ga musulman Najeriya su goyi bayan sake zaɓar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

A bayanin sun ce “rahoton ba gaskiya ba ne don sarkin musulmi uba ne ga kowa, ba zai yiwu ya faɗi haka a bainar jama’a ko wata haɗuwa ba”.

Prince Bashir Adefaka ya fitar da bayanin madadin masu kula da harkokin yaɗa labarai na Sarkin Musulmi a ranar Talata ya yi kira ga mutanen Nijeriya a kowane ɓangare na al’umma su nisanta kansu tare da yin tir da irin wannan ƙarya da rashin kishin ƙasa da ƙoƙarin taɓa martabar Sarkin Musulmi, a sawo shi cikin siyasar jam’iyya saboda wata buƙatar ƙashin kai.

Bayanin ya ce “a bayyane yake masarautar da Sarkin Musulmi yake jagoranta shi Uba ne yana nan kan matsayin, iyakarsa da ‘yan siyasa sanya masu albarka da ba su shawara ga duk wanda ya buƙaci haka.

“Ƙofar Sarkin Musulmi buɗe take ga kowa ba ruwansa da bambancin jam’iyya, kowa na shi ne zai cigaba da zama haka.”

Ya ce mutane su jefar da maganar, ba daga Sarkin Musulmi ta fito ba, ba shi da ɗan takara guda da yake goyon bayansa a zaɓen 2027. Zamansa na uba ga kowa ya himmatu wajen samar da zaman lafiya, haɗin kai da ɗorewar samun fahimtar juna a tsakanin mabiya addinai a Najeriya.

Ya yi kira ga manema labarai su riƙa bincike kafin yaɗa labarai su daina jefa mutane cikin ruɗani da jefa sarakuna cikin harkokin siyasar jam’iyya don haifar da ruɗu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here