Mun Kori Shugabar Mata Kwana Daya Kafin Ta Fitar Da Takardar Barin Jam’iya---PDP

Mun Kori Shugabar Mata Kwana Daya Kafin Ta Fitar Da Takardar Barin Jam’iya---PDP

Jam’iyar PDP a jihar Sakkwato ta bayyana korar shugabar mata ta jam’iya Hajiya Kulu Abdullahi Rabah kan zargin ta da yi wa jam’iyar zagon kasa da yin angulu da kan zabo.

A takardar da shugaban jam’iya a karamar hukumar Rabah Alhaji Mu’azu Dutsi Rara ya fitar ya ce a sakamakon kwamitin zatarwa na mazabar Rabah karkashin jagorancin Bello Kofar na dakatar da Hajiya Kulu Rabah mun amince da wannan hukuncin na dakatar da ita daga jam’iya.

Jami’in hulda da jama’a na jam’iyar PDP Hassan Sahabi Sanyinnawal a zantawarsa da Managarciya ya ce majalisar zartwar ta jam’iya ta amince da abin da karamar hukuma suka yi ‘mun kori  shugabar mata kwana daya kafin ta fitar da takardar barin jam’iya,  an same ta da yi wa jam’iya zagon kasa, za a maye gurbinta bayan kammala zaben Gwamna’, a cewar Sanyinnawal.

 Tsakanin takardar Kulu Rabah da Mu'azu Dutsi sun ci karo da juna domin shi ya bayyana ya karbi takarda ne daga shugaban mazabar Rabah yayin da ita kuma ta aikawa shugaban mazabar Maikujera takaradar sheda masa ficewarta daga jam'iya, abin da ke nuna cewa a tsakaninsu akwai wanda bai san mazabar da yake ba. Tau ko ma mine ne dai siyasa ce ake yi a tsakaninsu.