Ministan Kwadago na Nijeriya ya rasa mahaifiyarsa da shekara 93

Ministan Kwadago na Nijeriya ya rasa mahaifiyarsa da shekara 93

 
Ministan Kwadagon Nijeriya Alhaji Muhammmad Maigari Dingyadi ya yi rashin mahaifiyarsa Hajiya Hauwa'u  jiya Alhamis bayan ta yi jinya tsawon lokaci.
An yi mata janaza a ranar Jumu'a da safe gidan Ministan dake unguwar Polo a birnin Sakkwato.
Gwamna Sakkwato Ahmad Aliyu ya yi gaisuwar margayiyar a wani bayani da Sakataren yada labaransa Abubakar Bawa ya fitar a kafar sada zumunta ta Facebook ya ce gwamna ya bayyana kaduwarsa da rashin mahaifiyar ministan Kwadago da aikin yi Muhammad Maigari Dingyadi.
"Rasuwar Hajiya Hauwa'u rashi ne da ke taba zuciya tabbas mun yi rashi uwa abin son mu"
Hajiya Hauwa'u ta rasu tana da shekarru 93 ta bar 'ya'ya biyu da jikoki da dama.