Mataimakin Gwamnan jihar Sakkwato Honarabul Manir Muhammad Dan’iya Walin Sakkwato tun sanda ya zama mataimaki gwamna, a duk shekara yakan biya kudin shafi daya mai kala a jaridar Daily Trust ya taya Sarkin Musulmi murnar zagayowar ranar haihuwarsa, kan tsawon shekarun da ya yi a duniya lafiya lau a cikin jagorantar jama’a da yi masa fatan alheri.
Kamar yadda ya yake yi sama da shekara biyar wannan ya zama wata al’ada ta yi wa Sarkin Musulmi kara a wannan haujin, in da mutane musamman masana da masu bibiyar harkokin yau da kullum ke yin sam barka da wannan karar dake fitowa a wurin mutum mai daraja ta biyu, a jihar da Sarkin Musulmi ke jagorantar al’ummar Nijeriya gaba daya.
Wannan abin da yake masa kwarai yake kara daga kima da darajar masarauta a idon Duniya ganin yanda ake yi wa Sarkin Musulmi Sadaukarwa, hakan na nuna yanda yake zaman lafiya da masu mulkin jihar wanda abin so ne ga tafiyar sarauta kowace iri.
A gefen Sakkwatawa masu bibiyar lamurran yau da kullum wannan karimci yana share hawayensu ganin yanda zuma ke yi wa kanta zaki, kenan masu mulki a Sakkwato za su yi kowace sadaukarwa kan Sarkinsu, wannan sauke faralin nasu yana janyo wasu a jihohin Nijeriya biyo bayan su don su yi mustahabbi ganin ba wanda yake jiransu Sarki yana da gata a jiharsa.
Kwatsam wannan shekarar mai aiki ya dakatar da aikinsa MANAGARCIYA ta yi rabon ido tare da ba da cigiyar taya murnar Walin Sakkwato ga Sarkin Musulmi ta cika shekara 66 a jaridar Daily Trst ba a samu wanda ya ci karo da ita ba, abin da ke nuna a wannan shekarar kam an tafi hutu, sai dai abin ba a sani ba hutun na wuccin gadi ne ko na har abada ne?.
Don sanin abin da ya hana sanya wannan tallar a wannan shekarar duk kokarin jin ta bakin Walin ko wani na kusa da shi lamarin ya faskara domin ba a samu wata nasara ba.





