MEE'AD:Labarin Soyayya Mai Rikitarwa
_*MEE'AD*_
*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*
( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS )
P.W.A
*THE BOOK IS WRITTEN*
*BY*
*_HAUWA IBRAHIM MISAU_*
Wattpad__@hauwancyy44
_____GODIYA
Dukkan yabo da godiya su tabbaga Allah madaukakin sarki mai kowa mai komai daya bani ikon rubuta wannan littafi tsira da Aminci su kara tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad S, A, W.
JINJINA & SADAUKARWA
Na jinjina na kuma sadaukar da wannan littafin na gareki babbar aunty SAFNA ALIYU JAWABI Allah ya kara daukaka, basira da kuma fasaha ya kuma kareki da sharrin dukkan mai sharri. Ameeen .
*Page* 1️⃣
______Zaune take bisa kan kujera a falo hannun ta rike da cup da alama tea
take sha. sanye take cikin wata doguwar riga mara nauyi mai launin ruwan ganye.
fiskarta ɗauke da murmushi wayace rike a hannunta kirar infinix hot 10 tana dannawa da alamun chat take yi, fuskarta sai fitar da wani kyakkyawan murmushi yake kallo ɗaya zaka mata ka fahimci tana jin daɗin chatting ɗin da take sosai.
Batayi auni ba taji an ɗaka mata duka ta baya, a hansale ta juyo kasancewa abin sa tafi tsana kenan a rayuwarta.
"Ke wai mike damun kine?" kin girma, amma kin kasa gane hakan, to bana son irin wannan wasar dan haka karki ƙara "
Cike da mamaki Amal ta taɓe fuska tace" *MEE'AD* ba'a taɓa yi miki abin arziki wallahi kullum sai kin gwale mutane, karki mance na girme miki nisa ba kusa ba, dan haka zancan girma ma ki aje shi gefe sai kace ban girme miki ba," ta
Kawar da fuska gefe tayi gefe dan kuwa kamar zatayi kuka take ji tace" Ni dai kawai wasar ne bana so dan Allah ki daina, kinji Yayata?"
Murmushi Amal tayi tace" Albishirin ki"
"Goro fari tas"
"Gidan su Amrah zamu tafi yanzu"
"Tsalle tayi cikin zumuɗi tace "Dan Allah?"
"Wallàhi kuwa Hajiya zamu karɓowa saƙo"
mu"
"Kai wallahi naji daɗi bara na nayi wanka"
"To sarauniyar azarɓaɓi ba yau bane ba sai gobe"
Taɓe fuska tayi tace"Kai amma banji daɗi ba, wallàhi na ɗauka yau zamu tafi"
"Idan da rai ai gobe zata zo, amma wai drive ne zai kai mu"
"Kash Kinji Hajiya da wani irin magana kuma ko?"
"Rigimar ki da yawa take, to ƙwantar da hankalinki da kaina zan kai mu in sha Allah"
" Gaskiya naji daɗin hakan kinga bari naje na kwanta, dan so nake na tashi da wuri"
da wuri dan na tashi da wuri muji dadin
Rike da hannun juna suka shige cikin suna masu farin cikin gobe zasu ga Amrah....
*- Page -* 2
Amal ki tashi kiyi sallan asuba, mee'ad ce ke knocking kofar dakin Amal", daga cikin daki Amal ce kwance bisa kan bed lullube da lallausan blanket sai juyi take " cikin alamun bacci, Amal taja tsaki, kafin tace sai wani damun mutane kike to naki tashi din ta kara jan blanket taci gaba da baccinta.
"Mee'ad da ta gaji da knocking komawa room dinta tayi tadau HISNUL MUSLUM tafara karanta morning azkhar kamar yadda ta saba 'a kullum.
Mee'ad kinga na gama shiryawa , idan kin fito daga bath room ki sameni a darning na gaji da jiranki , daukan wayarta tayi ta fice ta nufi falo.
" Ta samu mutanen gidan zaune bisa darning suna break fast, a hanzarce Amal ta karasa ta tabe fiska, kafin tace mom shine baxaku jiramu muyi break din tare bako?" hararar ta mom tayi kafin tace kunji ya' wato sai mu tsaya jiranku sai time din da kukaga dama kuxo muyi break ko ?"
Amal tadan sosa kai, kafin taja kujera ta xauna a gefen dad",
" Murmushi dad yayi kafin yace kiyi hakuri yar daddy, baxa'a kara break a cikin gidan nan ba sai an jiraku, kinji yar daddy ?" gyada kai Amal tayi tana murmushin jin dadi, Dad yace ina mommy nane ta shiga ?"
Amal ta tabe baki, kafin tace tana sama har yanxu bata gama shiryawa ba, kasan halin maman naka ai Dad!
Abba dake gefensu ya tari numfashin Amal da sauri yana cewa bar mamana ta shirya 'a nitse bance ki tabamin ita ba",
" Tabe baki ta karayi kafin tace nifa Abba ba komai nace ba, murmushi Abba yayi kafin yace kima ce komai din kiga yanda xanyi dake .
"Umma tace wai miyasa kuke son takura ma yata ne ?" ku kenan kullum sai kun tabamin ita,gaskiya baxan lamunci hakaba,
"Amal tai dariya, kafintace yauwa Hajiyata, kice musu su daina takurani akan waccar yarinyar " hararar ta Dad yayi kafin yace mommyn tamuce yarinyar ?"
Amal tace Dad ai idan mom dinkune niba mom dina bace, Abba yace ke hingonki anan"!
"Gaba dayansu sukayi dariya cikin jin dadi kafin suci gaba dayi break dinsu hankali kwance....
*_ Page -* 3
A can bedroom kuma bayan Mee'ad ta fito daga bathroom tabi dakin da kallo bataga 6tern nata ba taja dan guntun tsaki mtsw! kafin ta tambayi kanta badai Amal ta rikani fita darning ba ? Bata da amsar tambayan haka taja baki tayi shiru.
Ta isa bakin dress mirror tadau mai ta fara shafawa cike da farin cikin yau zasuje gidan su Amrah".
"Ta gama shiryawa tsaf ta fito cikin shigarta mai kayatarwa", sanye take cikin wata doguwar rigar atampha kirar holland mai launin blue da ratsi white a jiki ba 'abinda take xubawa sai wani dadda dan kamshi,"
"Fiskarta dauke da murmushi ta sauko daga kan steps," kafin ta karasa sauka tayi arba da Amal zaune bisa kujera a falon kasa tasa Tv a gaba da remote a hanunta da alama ba Tv take kallo ba sbd fiskarta ya nuna kamar tinani take,"
Mee'ad ta karaso tadan dafata kafin tace waike mike damun kine ? naga kin wani xauna kina tinani cikin tsokana tace ko kina tinanin yayane ?"
"Amal taja wani gwauron numfashi ta tabe baki kafin tace sai akace miki haka kawai sai na xauna ina wani tinanin yaya, toma wai mixanyi dashi ne ?" kokin manta da soyayyar yarinta ne a tsakani na dashi ? tonina ma manta da wani yayan da kike magana akan nasa",
"Mee'ad ta nisa cikin tsokana tace au' nikam ai nayi tsammanin tinaninsa kike, Amal tace aikine bai ishe kiba sai kiyi tayin maganar nasa ni kinga tafiya ta,"
"Ta yunkura xata mike Mee'ad ta rike hannunta kafin tace Allah ya huci xuciyarki rabin raina, daga wasa sai wani jin haushi?"
Amal tadan murmusa kafin tace dadina dake kin fiye tsokana wllh, Mee'ad tace ke dinne idan ba'a tsokane koba ba'a daidaituwa,"
"Murmushi Amal tayi kafin tace kije kiyi break now dan umma tace anjima xamu kai mata aikan, murmushi Mee'ad tayi kafin ta tashi ta nufi darning tana cewa kinga bari nayi sauri sbd mu isa da wuri...
*- Page -*4
Hajiya umma ta sauko daga steps hannun ta rike da leda tana cewa kuna inane yan mata ?" kunga kuxo ku tafi kada ku makara dan baniso kukai dare.
"Cikin hanxari mee'ad taxo ta karbi ledan dake hannun Hajiya umma kafin ta kalleta cike da farin ciki tace kawo umma mun hutar ce ki, murmushi umma tayi kafin tace kunga kuyi sauri ku dawo baniso kukai dare kunji ko ?" Amal dake gefe ta ce umma insha Allahu baxa mukai dare ba xamu dawo da wuri, umma tace to kuje Allah ya kiyaye suka amsa da Ameen suka fita a jere.
A motor park Amal ta dubi Mee"ad cike da tsokana kafin tace malama bake xaki driving din bako ? Mee'ad ta harareta kafin tace ba kince driver ne xai kaimu ba ? Amal tace tin yaushe na hana hakan Mee'ad tai murmushi kafin tace Allah ya shirya minke sisina ki kaimu kawai idan yaso saina dawo damu ko ? Amal tace ba matsala muje ko, tare suka shiga motar suna dariya kafin su tafi.
*- Tushen labari -*
Gidan Alhaji sa'ad imam babban gidane daya hada komai na abinda ya shafi jin dadin rayuwar duniya baki daya.
Alhaji sa'ad babban mashahurin dan kasuwane wanda kasuwancinsa ya shahara a daukacin kasar nan da kewaye musamman jahar kano saboda acan kasuwancin sa yafi yawa 'amma asalinsa dan bauchine kasuwancine ya kaishi kano kuma ya samu wajen xama a unguwar sharada har yayi aure ya auri Hajiya Hindatu wacce ake kiranta da Hajiya Hindu, shekarar su 1 da aure ta sami haifuwa ta haifi danta mai suna Aliyu haidar bayan shekara 3 ta kara haifan da namiji wanda ake kira da Hisham bayan haifuwan Hisham da shekara 5 aka haifi kanwarsu wacce ta xama last born din Hajiya Hindu.
" Haka sukaita renon ya'yansu har suka girma abinsu yayinda Aliyu yafi karfi tagurin kasuwanci shi kuma Hisham yafi karfi ta waje karatun boko amma shima yana taba kasuwancin sai dai baikai na yayansa Aliyu ba, yayinda karamar kanwarsu wacce taci suna Amina suna kiranta da meenal ta girma ta shiga makaranta tana kan karatunta cikin kwanciyar hankali.......
managarciya