MEE'AD LABARIN SOYAYYA MAI RIKITARWA:FITA TA ASHIRIN DA BIYU

MEE'AD LABARIN SOYAYYA MAI RIKITARWA:FITA TA ASHIRIN DA BIYU
                   
             
                
 
     
 
           
*BY*
 
*_HAUWA IBRAHIM MISAU_*
 
Follow me on wattpad
@hauwancyy44
 
  
 
 
         
      
 
****Wannan shafin kyauta ne gare ki ZAINAB YUSUF ISAH MISAU. Na gode da damuwar da kike yi wajen ganin nayi post akan lokaci bazan ta'ba mantawa da hakan ba. Ina alfahari da ke.
 
47 ~ 48
 
Ya 'kara wanka mata mari a karona uku, ya nunata da yatsa ke dama baki da kunya ko jikina ya bani hakan tin kafin azo wannan lokacin dan haka ban yadda ki kara shigowa part din nan ba har sai na baki izini ke !  in takaice miki zance ma na fasa aurenki da nace zanyi sbd na abinda na tsana a fad'in duniyar nan face mace mara kamun kai, tashi ki fita daga dakin nan.
 
"Dafa kunci Amal tayi sannan tabi fuskarsa da kallo, tuni hawayen ba'kin ciki ya wanke mata fuska, jiki a sanyaye ta nufi 'kofar fita " juyowa tayi fuskarta cike da ba'kin ciki ta ce Yaya kayi hakuri wllh hakan ba halina bane.
 
"Harara ya galla mata nace miki ki 'bace min da gani ko ? 
 
Ficewa tayi daga part din ba tare da tayi musu ba, kai tsaye bedroom d'inta ta nufa fuskarta cike da hawayen ba'kin ciki.
 
"Dogon tsaki yaja ya nufi kofar falon ya danna masa key ya dawo ya kwanta bisa kujera ya fara tinanin abinda ya faru tsakaninsa da Amal," Jinjina kai yayi cike da takaici yake fad'in lallai ma yarinyar ta raina min wayo, waima yaushe halinta ya koma hakane ? anya ba canzamin ita 'akayi ba ? wai Amal d'ita abar kaunata itace take irin wannan halin gaskiya ban yadda da hakan halayyarta bace.
 
Nan yaci gaba da surutu yana mai ~ maita sunan Amal, kuma yana mamakin canjuwar halayyar nata cikin lokaci 'kan'kani.
 
"Da guduta shiga bedroom d'in, fad'awa kana gado tayi ta fashe da kukan takaici, wash Allah na 'anya kuma Amrah tana bani kyakkyawan shawara kuma ? na lura da duk lokacin data bani shawara kan wani abu sai na samu matsala da 'abun, sa'bamin dacan da nake shawara da Mee'ad, anya zanci gabada bama Amrah dukka 'amincina kuwa.
 
"Ta 'kara fashewa da kuka cikin kukan take cewa bazan 'kara baki dukkan yarda taba Amrah, insha Allahu gobe da safe zanje gidansu Laila naji kalar tata shawaran.
 
%%%%%
 
Kwance yake bisa kujera sai juye-juye yake sakamakon ya kasa ritsawa baki daya tinanin abinda ya shiga tsakaninsu da Amal ya'ki ya bari hankalinsa ya kwanta. Wayarsa ya dauko yayi dealing number baban Abokinsa wato Saleeem.
 
"Bugu d'aya ya dauka barka da dare nawa y garin ? wato kai tinda ka koma kano ka daina neman mutane ko ? ko dai Amal d'ince ta hanaka kula manyan abokanka ? nafi tunanin Amal d'innan tanada muhimmmancin da zata aikata fiye da hakama."
 
"Shiru yayi bai tanka masa ba sai da ya gama y'an suruce ~ surucen sa.
 
"Gyara kwanciya yayi sannan yace to aku mai bakin zancen, surutun ya isa haka mana! ka nitsu ka saurareri abinda zan fad'a maka.
 
"Shiru Saleem yayi kafin ya ce ina jinka."
 
"Murmushi yayi kasan miyasa na kiraka da wannan daren?"
 
" A'ah Saleem yace "
 
"Ya d'anyi shiru na wasu lokuta kafin yaci gaba da cewa, tin lokacin dana dawo 'kasata nigeria Amal ta yaye kulawar da take bani kullum tana kan 'batamin rai da hargitsamin tinani, gaba d'aya abin sai damuna yakeyi, in takaice maka dazu da tazoma...."
 
"Nan ya fad'a masa dukkan abinda ya faru tsakaninsu "
 
Saleeem ya fashe da daria sai da yayi mai isarsa kafin dai ~ daita kansa yace oh sorry brother abinne yad'an bada citta shiyasa na kasa d'aurewa saida na dan dara".
 
"Majeed a fusace yake fad'in wai kai shashshashan wani garine da ina fad'a maka 'abinda ke damuna kana wani daria! Allah zan kashe wayata idan bazaka nitsuba." 
 
Saleem ya daina daria sbd yasan halin abokin nashi sosai, nisuwa yayi kafin ya ce kasan mina fahimta a wannan labarin daka banin ? to Amal dai tayi haka dan ta gwada kane, kuma bawai bata kaunarka bane kawai tanada matsiyacin kishine, amma zamu fito mata ta bayan gida, ka daina kulata ka nuna mata kai da gaske ka fasa ' auren nata, sannan ka shirya kayanka tsaf ka dawo yola ranar sunday ka fasa cika sati 2. 
 
" Murmushi yayi Abokina miye hikimar ka na cewa na taho ranar sunday ?
 
Daria Saleem d'in yayi! idan har ka taho tanan zaka gane wani irin soyayya take maka dan zata iya hakura da karatun da takeyi ta biyoka, kod'an ka yafe mata abinda tayi maka.
 
Murmushin jin dad'i Majeed yayi sannan yace godiya nake Abokina, zanyi iya bakin 'ko'karina naga na dauki shawarar ka, duk dama zanyi kadaicin Mee'ad amma ya zama dole na dawo yola cikin week din nan ma.
 
"Saleem ya gyara zama Abokina wacece kuma Mee'ad ?
 
Majeed tashi yayi ya zauna dan yaji an ambaci sunan kyakkyawar 'Kawarsa, nan ya fara bashi labarin Mee'ad d'in, sai da ya kammala bashi labarin kafin yayi shiru.
 
"Saleem ya 'kara fashewa da daria abokina kace soyayya biyu kakeyi abinka ? 
 
Majeed ya ce soyayya biyu kuma ? ba soyayya biyu nakeyi ba kawai Mee'ad tafi bani kulawa   ta kuma fi Amal kula dani dabin dukkan abinda nakeso kai na takaice maka zancen ma Mee'ad ta musamman ce dan har abincin da nakeso tin tana yarinya ta sani kuma har yau bata manta ba.
 
Shege kaya! nifaa ban yadda da wannan Mee'ad d'in ba gaskiya kawai zuciyarka tana soyayya guda biyune amma nasan bazaka fiskanci hakan ba sai nan gaba... Nan dai sukaci gaba da firansu suna daria har dare yayi sosai kafin sukai sallama da juna.
 
Karfe takwas dai ~ dai agogon dakin Amal ya buga cike da hanzari ta nufi toilet danyin wanka sbd ta kwana da burin zuwa gidansu 'kawarta Laila.
 
Bata d'auki lokaci ba ta fito sallah asuba tayi kafin ta shirya ta nufi bedroom d'in Umma ina kwana Umma yau inaa sauri zan shiga lectures 9 kuma inson zanje gidansu Laila kinsan an kawo lefenta zanje na yini acan zan kuma ga lefen nata.
 
Murmushi Umma tayi ba matsala Allah ya kiyaye hanya, amma kici wani abu kafin ki wuce school din kinji ?
 
To tace kafin ta nufi kofar fita a hanzarce.
 
Kitchen ta nufa Inna hadamin break a wannan kular zan tafi makaranta dashi yanzu,"
 
Inna ta had'a mata abincin karyawa a kula ta mika mata tana cewa Allah ya kiyaye hanya Hajiya"
 
Murmushi Amal tayi na gode Inna sai na dawo, da gudu ~ gudu ta nufi kofar fita daga falon ko kallon gabanta batayi sbd sauri ki tayi ta buge mutum a tsorace ta d'ago kai wa zata gani Majeed ne tsaye bakin kofar sanye da ba'kar jallabiya fuskar nan a had'e babu annuri."
 
" Jiki a sanyaye tace sorry Yaya ban ganka bane,"
 
"Harara ya galla mata kafin yaja tsaki mtswww! ke wacce irin y'ar wawuya ce da zaki buge mutum kina kallo......? 
 
Cike da tsiwa Amal tace to dana buge mutumin bance yayi hakuri bane ? 
 
"Kaga Malam dan wani abu ya kasance tsakanin mu baza kazo ka raina mini hankali ba ehee! tana gama fad'in haka ta nufi harabar gidan tana yatsine fuska.
 
"Ya bita da mungun kallo sanna yayi kwafa ya shiga cikin gida.
 
 
 
 
 
 
pls 
 
Follow 
 
Share
 
Vote
 
Comment
 
Fisabilillah.