Matsin Rayuwa: Tinubu Ya Nuna Gamsuwa Ga Tsare-Tsaren Tattalin Arzikinsa

Matsin Rayuwa: Tinubu Ya Nuna Gamsuwa Ga Tsare-Tsaren Tattalin Arzikinsa
Daga Nabila Khamis
Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ta tsaya tsayin daka wajen aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da suka dace don saukaka cigaban kasuwanci da samar da damar zuba jari da ke tallafawa  al’ummar Najeriya.
 
A yayin da yake karbar tawaga daga kungiyar kasuwanci CCA a karkashin jagorancin shugaban Kungiyar kuma babban jami’in gudanarwa Florizelle Liser,  a Abuja ranar Alhamis, shugaba Tinubu ya jaddada aniyarsa na ganin ya bunkasa tattalin arzikin Najeriya da kuma kawo kwanciyar hankali, yana mai jaddada cewa ba zai ja da baya ba har sai burinsa ya cika ga 'yan Najeriya.
 
 Shugaban Kasar ya yi nuni da cewa,idan aka samar da ingantattun manufofi, haɗin gwiwa, da azama, Najeriya za ta iya shawo kan matsalolin  da ta daɗe tana fuskanta. 
 
Shugaba Tinubu ya kara jaddada kudirinsa na sake kirkiro da sabbin hanyoyi don bunkasa kasuwanci, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen saka hannun jari a muhimman sassa daban daban, kamar noma, ma'adanai, makamashi, lafiya, kayayyakin more rayuwa, inganta kasuwanci, hidimar hada-hadar kudi, kasuwanci na zamani, da sauransu. tattalin arzikin kirkire kirkiren zai dogara ne domin  tabbatar da walwala da jin dadin 'yan kasa.