Matsalata da Saraki da Tambuwal ---Wike

Matsalata da Saraki da Tambuwal ---Wike

Gwamnan jihar Rivers Wike ya bayyana dalilinsa da ya sanya yake da matsala da 'yan takarar shugaban kasa da suka fito daga Arewacin Nijeriya Sanata Bukola Saraki da Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal kan mayar da takarar shugaban kasa a Kudancin Nijeriya ne a 2023.

Wike ya fadi haka ne a ranar Litinin ya ce a koyaushe yana goyon bayan dan takarar shugaban kasa daga Arewa bai ga dalilin wadanda suka nemi a tsayar da su a 2019 kuma su sake ddawowa a 2023 ba.
Ya ce ya goyi bayan Tambuwal ya zama kakakin majalisar tarayya, haka ma Saraki da ya zama shugaban majalisar dattijai bai kula da duk wani da ke iya tasowa ba.

Wike ya fahimci gwamnan Benue ne kawai yake goyon bayan takararsa daga cikin gwamnoni ya ce mutanen Nijeriya ba su son su fadi gaskiya wannan abin takaici ne.